Tsohon Gwamna Ya Fallasa Makarkashiyar da Ake Yi wa ‘Ya ‘Yan PDP Daf da Zaben Jihohi
- Ahmed Muhammad Makarfi yana zargin cewa ana bi ana cafke magoya bayan PDP a Kaduna
- An ji tsohon gwamnan jihar Kaduna ya fitar da jawabi, yana cewa ana so a kama masu mutane 80
- Sanata Ahmed Makarfi ya ce an tsare wani Hon. Shehu Adamu ba tare da an fadi laifin da ya yi ba
Kaduna - Tsohon gwamna a jihar Kaduna kuma jigo a tafiyar PDP, Ahmed Muhammad Makarfi ya ce ana kokarin cafke wasu ‘yan jam’iyyarsu.
A rahoton da aka fitar a Daily Trust, Sanata Ahmed Muhammad Makarfi ya ce ana cafke ‘ya ‘yan PDP ne saboda kurum a hana su shiga zaben Jihohi.
Ahmed Muhammad Makarfi wanda ya yi Gwamna a jihar Kaduna tsakanin 1999 da 2007, ya ce magoya bayan Jam’iyyar PDP su 80 ake shirin a cafke.
A Karshe Wike Ya Bayyana Wanda Ya Kori Peter Obi Daga PDP A Yayin Da Rikicin Jam'iyyar Ke Kara Ruruwa
Kawo yanzu, tsohon Sanatan ya ce jami’an tsaro sun yi ram da wasu manya-manyan ‘yan PDP uku a jihar da sunan sun yi kalaman da ke iya tada fitina.
An cafke Kakakin kwamitin kamfen PDP
Rahoton ya ce tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na kasan ya maida martani a game da cafke Saidu Adamu da wasu jagororin PDP da jami’an tsaro suka yi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Saidu Adamu shi ne Darektan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben PDP a jihar Kaduna.
Dauki dai-daya a wasu garuruwa
This Day ta ce a jawabin da Sanata Ahmed Makarfi ya fitar, ya ce ana yunkurin kama ‘yan PDP a garuruwan Kudan, Sanga, Igabi, Lere, Kachia da Jaba.
Makarfi ya ce ana neman ayi wa mutanensu dauki daya-daya a karamar hukumar Kaduna ta Arewa, wadannan su na cikin inda PDP ta ke da karfi.
“Har yanzu Honarabul Adamu yana garkame kuma ba mu san laifin da ake tuhumarsa da aikatawa ba, abin takaicin shi ne ana tsare shi, ba a kai shi kotu ba.”
- Ahmed Muhammad Makarfi
An kama masu sukar takarar Musulmi da Musulmi
Rahoton ya ce a cikin wadanda aka kama saboda sun yi kalamai na suka a kan tikitin Musulmi da Musulmi akwai Abbas Mohammed da Talib Mohammed.
Wannan ya sa Makarfi ya gargadi jam’iyyar APC mai mulki a kan zaluntar ‘yan adawar siyasa.
Lamarin Abbas Senior
Legit.ng Hausa ta zanta da Fahad Sani Abdullahi wanda 'danuwa ne ga Alhaji Abbas Senior wani shugaba na PDP a yankin Kabala da aka yi ram da shi.
A ranar Talata jami'an tsaro suka shiga gida suka dauke wannan Bawan Allah, Fahad ya shaida mana cewa dazu aka fito da jagoran jam'iyyar hamayyar.
Majiyarmu ta ce ba a shigar da karar shugaban na kungiyar National Mandate Group na shiyyar Kabala a gaban kotu ba, duk da an yi yunkurin yin haka a jiya.
Za a gyara PDP - Wike
An ji labari Gwamna Nyesom Wike yana cewa sun gama yakin farko, za a shiga gumurzu na biyu a PDP domin a kora mayu da masu kahon-zuka.
Bayan an kafa sabuwar gwamnati a Mayun 2023, Mai girma Wike ya ce za su karbe jam’iyyar adawa ta PDP daga hannun wadanda suka tsere a 2015.
Asali: Legit.ng