Da Sauran Rigima, Gwamna Wike Ya Jero Wadanda Za a Fatattaka Daga Jam’iyyar PDP

Da Sauran Rigima, Gwamna Wike Ya Jero Wadanda Za a Fatattaka Daga Jam’iyyar PDP

  • Nyesom Wike ya ce dole ayi waje da wadanda suka taimaka wajen bada tikitin PDP ga Atiku Abubakar
  • Gwamnan Jihar Ribas ya nuna za a fara wani sabon rikici a Jam’iyyar PDP bayan an canza gwamnati
  • Wike yana ganin an saba tsarin Jam’iyya da aka tsaida ‘Dan Arewa ya yi takarar shugaban kasa a 2023

Rivers - A tsakiyar makon nan aka ji Gwamna Nyesom Wike yana bayanin yadda za a kawo gyara a jam’iyyar PDP bayan an yi canjin gwamnati.

The Cable ta rahoto Nyesom Wike yana cewa za su kora miyagu da masu zukar-jini daga jam’iyyarsu, yana cewa za a sake gina PDP daga farko.

Mai girma Gwamnan yana fada da jagorancin Iyorchia Ayu wanda a karkashin aka ba Atiku Abubakar takarar kujerar shugaban kasa a zaben bana.

Kara karanta wannan

Yadda Tambuwal da Shugabannin PDP Suka Haddasa Shan Kashin Atiku – Jigon PDP

Da ya je bude wani titi mai kilomita 10 da ya gina a garin Igwuruta da ke karamar hukumar Ikwerre, Nyesom Wike ya ce za ayi wa PDP garambawul.

Kokarin 'Yan G5 a PDP

Gwamnan ya yi bayanin yadda ‘yan tawagarsa ta G5 suka yi kokarin ganin an tsaida mutumin Kudu a matsayin ‘dan takaran shugaban kasa a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ta ambato Wike yana cewa wadanda suka sabawa tsarin mulkin jam’iyya na karba-karba za su yabawa aya zaki, domin za a kore su daga PDP.

Nyesom Wike
Gwamna Nyesom Wike Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mun gama yakin farko. Za mu shiga gumurzu na biyu. A yaki na biyu, dole mu kora mayu da masu kahon-zuka, za mu fatattake su daga PDP.
Za mu karbe jam’iyya, mu gyara ta. Wadannan mutane sun bar jam’iyyar a 2014/15 da muka rasa zabe, yanzu sun dawo, mun sake rasa zabe.

Kara karanta wannan

Ba za ku iya taimakon Atiku ba: Shehu Sani ya bi kan su Wike, ya yi musu wankin babban bargo

Sun lalata jam’iyyar, za mu kore su daga jam’iyyar. Ba su da wata rawar da za su iya takawa."

- Gwamna Nyesom Wike

Wike ya soki Amaechi, Abe

The Nation ta rahoto Gwamnan na Ribas yana zargin Rotimi Amaechi da Magnus Abe da yaudar kungiyar Kiristoci na CAN da Inyamuran da ke Ribas.

A cewar Wike, Amaechi yana kokarin tallata Tonye Cole a yankin Inyamurai, yayin da Abe ya yi wa CAN alkawarin zai kai Kiristoci Israila idan aka zabe shi.

An rasa 'Dan NWC a APC

A wani rahoto da mu ka fitar a karshen makon nan, an ji daya daga cikin ‘Yan Majalisar NWC a Jam’iyyar All Progressives Congress ya rasu a asibiti.

Friday Nwosu wanda shi ne Sakataren walwalan APC na kasa ya rasu ne bayan ya yi fama da ‘yar gajerar rashin lafiya a Abuja, kuma ya fara samun sauki.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Ƙara Rikita Lissafin APC Ana Dab da Zaben Gwamnoni a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng