Labari Mai Zafi: Babban Wakilin Atiku a Zaben 2023 Ya Rabu da Shi, Ya Koma APC

Labari Mai Zafi: Babban Wakilin Atiku a Zaben 2023 Ya Rabu da Shi, Ya Koma APC

  • Johnson Fatoki ya gaji da zama a Jam’iyyar PDP, ya sauya-sheka zuwa APC mai mulki a kasar
  • ‘Dan siyasar da wasu mutanensa sun sauya-sheka zuwa wajen Dapo Abiodun mai harin tazarce
  • A zaben Shugaban kasa da aka yi, Fatoki ya wakilci Atiku Abubakar wajen tattara kuri’un Ogun

Ogun - Johnson Fatoki wanda ya yi aikin wakilin zabe na jam’iyyar PDP a takarar shugaban kasa a jihar Ogun, ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.

A ranar Alhamis, Daily Trust ta rahoto Johnson Fatoki ya bar PDP zuwa jam’iyya mai mulki, hakan na zuwa ne kwanaki bayan zaben shugaban Najeriya.

‘Dan siyasar ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC ne yayin da ake shirye-shiryen karshe na zaben Gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki na jihohi a kasar.

A wajen tattara kuri’un jihar Ogun, rahoton ya ce Fatoki ya wakilci Atiku Abubakar wanda ya nemi takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Zababbun ‘Yan Majalisa Masu Neman Shugabanci a Majalisar Wakilai da Dattawa

Gwamnan Ogun ya yi kamu

Sauya shekar ‘dan siyasar ta zo ne a daidai lokacin da ‘yan adawa su ke komawa bangaren Gwamna Dapo Abiodun wanda yake neman tazarce.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauye-sauyen shekar da ake yi a Ogun ya zama tamkar an bude kasuwar cefanen ‘yan siyasa.

'Yan APC
Magoya bayan Abiodun Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Fatoki ya amsa kira a Iperu-Remo

Fatoki wanda tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Ogun ne, ya shaidawa mutanen Iperu-Remo cewa an matsa masa ya bar PDP.

Da yake bayani a mahaifar Gwamnan Ogun, ‘dan siyasar ya ce shi da mutanensa sun koma tafiyar Mai Abiodun bayan zawarcinsu da jam’iyyu suka rika yi.

An rahoto Faytoki yana cewa su na tare da kwararrun ‘yan siyasa daga jam’iyyu dabam-dabam daga Ogun ta tsakiya da ke goyon bayan APC ta zarce.

A cewarsa, ba su neman komai a wajen Gwamna mai-ci, sun zo ne kurum su bada gudumuwarsu domin sun san ko babu su, APC za ta lashe zaben jihar.

Kara karanta wannan

Rudani: Saura kwanaki zabe, an sauya kwamishinan 'yan sanda a jihar Arewa bisa zargin hannu a siyasa

PDP ta rasa 'ya 'yanta a Ogun

Baya ga Fatoki, kusoshin jam’iyyar hamayyar da suka tsallaka zuwa APC a ‘yan kwanakin nan sun hada da Segun Seriki da Otunba Femi Osifade.

Haka zalika Alhaji Saula Adegunwa, Ralph Olaosebikan da Tola Mebude da aka sani a jam’iyyar PDP, duk sun koma tare da Gwamna Abiodun a APC.

Siyasar Kaduna a 2023

A wani rahoto na musamman, kun ji tarihin Sanata Uba Sani wanda ya taba zama mai bada shawara a harkokin siyasa mai takara a Kaduna a APC.

Sannan Hon. Sani Mohammed Sha'aban, Jonathan Asake da tsohon Hadimin Gwamna Nasir El-Rufai, Hayatu Makarfi duk su na takara a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng