‘Yan Takara 6 da ke Hangen Kujerar El-Rufai a APC, PDP, LP, NNPP, ADP da PRP
Kaduna -A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta tattaro wadanda suke takarar kujerar Gwamna a jihar Kaduna, kuma ana tunanin daga cikinsu za a samu Gwamnan gobe.
1. Uba Sani
Uba Sani shi ne ‘Dan takaran Gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC. Sanatan mai shekara 52 zai zo ya zama magajin mutuminsa, Nasir El-Rufai.
Asalinsa mutumin Zariya ne, kuma ya yi digirinsa a bangaren Injiniyanci, daga baya ya yi digirgir a fannin tattalin arziki da PGD a kasuwanci a Kalaba da Abuja.
A 1999 Uba Sani ya zama Hadimi ga Shugaba Olusegun Obasanjo, bayan nan ya yi aiki da Nasir El-Rufai a FCTA a lokacin yana Ministan babban birnin tarayya.
A zaben 2011 ya nemi takarar Sanata amma bai samu tikitin PDP ba. Da El-Rufai ya zama Gwamna sai ya nada shi mai bada shawara a kan harkokin siyasa.
A karshe Uba Sani ya zama Sanatan Kaduna ta tsakiya bayan ya karbe tikitin Shehu Sani, ya kuma lashe zabe. A 2023 aka tsaida shi a matsayin ‘dan takarar Gwamna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Rt. Hon. Isa Ashiru Kudan
Hon. Isa Ashiru Kudan yana neman kujerar Gwamnan Kaduna a jam’iyyar PDP. An haifi Sarkin Ban Zazzau ne a 1962, ya yi karatunsa tsakanin Kaduna da Kano.
Isa Ashiru Kudan ya samu Difloma a 1985 a harkar kula da kasuwanci, a 1989 ya yi nasarar samun babbar difloma, yana da shaidar Digirgir daga jami’ar BUK a 2001.
Bayan aiki a Ma’aikatun kudi da na kasuwanci na jihar Kaduna da Hukumar tatsar kudin shiga, Kudan ya rungumi siyasa gadan-gadan da aka dawo farar hula a 1999.
An zabi Isa Ashiru Kudan a matsayin ‘dan majalisar dokoki na jihar Kaduna. A shekarar 2007 ya zama ‘dan majalisar wakilan tarayya, a nan ma ya yi shekaru takwas.
Bayan kafa jam’iyyar APC sai ‘dan siyasar ya bar PDP, ya nemi tikitin zama Gwamna a 2014, daga baya ya koma PDP har ya nemi Gwamna a 2019, bai dace ba.
3. Jonathan Asake
‘Dan takaran jam’iyyar LP a zaben Gwamnan jihar Kaduna a zaben bana shi ne Jonathan Asake. Tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayyar zai gwabza da APC da PDP.
Kamar yadda LP tayi karfi a Kudancin Kaduna, Asake ya fito daga yankin ne, har ya taba rike shugabancin kungiyar SOKAPU kafin ya dawo harkar siyasa a 2022.
4. Suleiman Hunkuyi
Suleiman Othman Hunkuyi mai shekara 63 yana neman kujerar Gwamnan Kaduna a jam’iyyar NNPP. Masu nazarin siyasa su na ganin yana bayan APC da PDP.
Suleiman Othman Hunkuyi ya yi digiri daga jami’ar ABU Zariya a 1986. Bayan ya gama karatu ya shiga siyasa har ya zama shugaban karamar hukumarsa ta Kudan.
Tsakanin 2015 da 2019, Hunkuyi ya wakilci Arewacin Kaduna a majalisar dattawa. ‘Dan siyasar yana cikin Sanatocin da suka bar jam’iyyar APC kafin zaben 2019.
Ba wannan ne karon farko da Sanatan ya nemi takarar Gwamna ba, ko a 2019 ya shiga zaben fitar da gwani na PDP, amma ya sha kashi a hannun mutumin yankinsa.
5. Sani Mohammed Sha'aban
Wani mutumin Zariya a cikin ‘yan takaran Gwamna a 2023 shi ne Sani Mohammed Sha'aban. ‘Dan kasuwan yana neman mulkin jihar Kaduna a karkashin ADP.
Kafin sauya-shekarsa zuwa jam’iyyar ADP, Sani Mohammed Sha'aban yana cikin wadanda aka kafa APC da su a Kaduna, ya fi shekaru 20 ana damawa da su a siyasa.
Tsakanin 2003 da 2007, Sha’aban ya wakilci mazabar Zariya a majalisar wakilan tarayya, bayan nan ya nemi takarar kujerar Gwamna a ANPP amma bai yi sa’a ba.
6. Hayatu Lawal Makarfi.
A jam’iyyar PRP Malam Hayatuddeen Lawal Makarfi yake neman Gwamnan jihar Kaduna, ya lashe zaben tsaida gwani da aka shirya a watan Yunin shekarar 2022.
‘Dan auta a cikin manyan ‘yan takaran ya yi karatu a makarantun Therbow, Turaki International da Zamani College, daga nan ya tafi jami’ar ATBU ta Bauchi a 2002.
‘Dan takaran na PRP ya yi aiki da Ahmadu and Partners Limited zuwa shigarsa siyasa a 2014 har ta kai ya zama Mai ba Gwamna Nasir El-Rufai shawara.
A farkon 2016 aka tura Makarfi zuwa KAPWA, Hukumar da ya zama mataimakin Manajanta. Bayan nan ya yi aiki a madaba'ar Belsha Printing Press da NFIU.
Siyasar jihar Legas
A wani rahoto da muka fitar, an ji labari zargi ya zo cewa ana kulle-kullen kashe ‘Dan takaran Gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar hamayya ta LP.
Bode George da ya taba zama mataimakin shugaban jam’iyyar PDP ne yake yada maganar cewa akwai masu shirin hallaka Gbadebo Rhodes-Vivour.
Asali: Legit.ng