Ministan Buhari Ya Fayyace Komai Bayan An Ga Babu Sunansa Cikin Lauyoyin Tinubu
- Da farko an yi tunanin Festus Keyamo SAN yana cikin Lauyoyin da za su ba Bola Tinubu kariya
- Lauyan ya ce tun da shi Minista ne, ba zai iya tsayawa ‘dan takaran ba sai ya sauka daga kujera
- Amma mutane sun shiga yi wa Keyamo raddi cewa yana kujerar Ministan, ya shiga siyasa
Abuja - Festus Keyamo wanda babban Lauya ne da ya kai matsayin SAN, ya dauki lokaci ya yi karin-haske a kan batun shari’ar zaben shugaban kasa.
Ganin cewa ba a ga Festus Keyamo SAN a jeringiyar Lauyoyin da za su tsayawa Asiwaju Bola Tinubu a kotun zabe ba, wannan ya jawo abin magana.
Lauyan ya yi amfani da shafinsa na Twitter a ranar Talata, ya fadi abin da ya ba zai iya kare ‘dan takaran APC kuma zababben shugaban kasar a kotu ba.

Kara karanta wannan
Ministan Buhari Ya Fadi Babban Dalilin Da Yasa Baya Cikin Manyan Lauyoyin Da Za Su Kare Tinubu
Keyamo ya nuna a matsayinsa na wanda yake rike da mukami a gwamnatin tarayya, bai da damar da zai shiga kotu domin ya ba daidaikun mutane kariya.
Babu ruwan Minista da karar zabe
Tun a 2019 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Lauyan a matsayin Minista a ma’aikatar Neja-Delta, daga baya ya koma ma’aikatar kwadago.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A daidai lokacin da yake Ministan gwamnati, Daily Trust ta rahoto masanin shari’ar yana cewa ba zai iya shiga kotu ba har sai ya sauka daga kujerarsa.

Asali: Facebook
Iyakar gudumuwar da Keyamo ko wani Minista da ya kai matakin SAN a Lauya zai iya ba Bola Tinubu a yanzu shi ne a wajen shirye-shiryen shiga kotu.
Maganar Festus Keyamo a Twitter
"Ga masu aiko da tambaya, a kundin tsarin mulkin kasarmu, Ministan tarayya mai-ci ba zai iya shiga cikin tawagar Lauyoyi masu zaman kan su ba.

Kara karanta wannan
Sabon Harin Zamfara Da Kano: Tinubu Ya Yi Allah Wadai, Ya Ce Dole a Takawa Kashe-Kashe Birki a Najeriya
Sai dai Ministan ya/ta taimaka wajen shiryawa shari’a. Saboda haka Ministocin da sun kai matsayin SAN ba za su iya shiga shari’ar zabe ba sai bayan 29 ga watan Mayu."
- Festus Keyamo
Irinsu Harry Iwuala ba su kyale kakakin kwamitin yakin neman zaben na APC haka ba, suka ce ai yana kan kujerar ya rike mukaman siyasa a kamfe.
"Minista mai-ci ya je kotu yana so a gurfanar da ‘dan takaran shugaban kasa. Minista mai-ci ya karbi mukami a kwamitin kamfe.
Shi ya rika yin kalaman siyasa da ba su dace da jami’in gwamnati ba. Ko kun san wanene wannan Minista?
- HARRY Iwuala
Rikicin PDP a Katsina
Yayin da ranar zaben Gwamnonin jihohi ya gabato, an ji labari ‘Yan PDP sun yi karar Sanata Yakubu Lado Danmarke da wasu daga cikin ‘yan bangarensa.
Shugabannin jam’iyyar PDP a Katsina su na tuhumar Aminu Yar’dua, da Mustapha Inuwa da zargi kan yadda aka batar da Naira Biliyan 1.05 na yin kamfe.
Asali: Legit.ng