INEC ta Bada Dalilin Cire Sunan Yaron Tsohon Gwamna Cikin Zababbun ‘Yan Majalisa
- Hukumar zabe ta INEC tayi waje da sunan Gboyega Adefarati a cikin wadanda za su tafi majalisa
- Gboyega Adefarati ya ga samu ya ga rashi a sakamakon karar da aka kai, aka ba APC rashin gaskiya
- Alkali ya ce APC ba tayi zaben tsaida gwani a Akoko ba, saboda haka ba ta da ‘dan takaran majalisa
Abuja - Hukumar zabe ta kasa watau INEC, ta janye sunan Gboyega Adefarati daga cikin wadanda suka samu nasara a zaben ‘yan majalisar tarayya.
The Cable ta ce yanzu babu sunan Gboyega Adefarati a cikin jerin zababbun ‘yan majalisar wakilai na kasa duk da an tabbatar da ya lashe zaben 2023.
‘Dan siyasar yana cikin ‘ya ‘yan Marigayi Adebayo Adefarati wanda ya yi Gwamna a jihar Ondo.
A zaben bana da aka shirya, Adefarati ya yi takarar kujerar ‘dan majalisar Akoko a majalisar tarayya, kuma ya samu yin galaba a karkashin APC.
APC ta samu babbar nasara
A baya baturen zaben da ya yi aiki a mazabar Akoko, Ibukun Emmanuel ya sanar da Adefarati a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u fiye da 25, 000.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sakamakon zaben ya ce APC ta doke ‘dan takaran PDP, Gbenga Kolawole da ya ci kuri’u 18,403. Kwatsam sai yanzu labarin yake neman ya canza.
Hukumar INEC mai shirya zabe a Najeriya ta ce an yi waje da sunan ‘dan takaran ne a dalilin hukuncin da Alkali ya yi, ya soke takarar da ya samu.
A ranar 17 ga watan Fubrairu, kotu ta ruguza zaben fitar da gwanin da ya ba Adefarati tuta. People Gazette ta ce APC ce ta ci kujerun majalisar Ondo.
Tirka-tirka a kotu
Mun fahimci tun a 2022 Segun Ategbole da John Adanike suka je kotu bayan zaben tsaida ‘dan takara da aka shirya, suka kalubalanci nasarar Adefarati.
Da rigima ta barke tsakanin masu neman tikiti a APC, sai Ogunleye Teloye mai takara a ZLP ya tafi kotu, ya nemi a hana APC shiga zaben bana gaba daya.
Mai shari’a T.B. Adegoke ya gamsu da korafin Teloye, ya ce jam’iyya mai mulki ba ta shirya zaben tsaida gwani ba, don haka ba ta da ‘dan takara a 2023.
Malamin zabe ya tona asirin komai
Ku na da labari Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya ce an yi wa rayuwarsu barazana wajen sanar da sakamakon zaben majalisar Tudun Wada da Doguwa.
Wasikar da Farfesan ya rubutawa INEC ya nuna da karfi-da yaji aka ba APC nasara. A yanzu batun tazarcen Hon. Alhassan Ado Doguwa ya shiga rububi.
Asali: Legit.ng