Yanzu Yanzu: PDP Ta Koka, Ta Zargi INEC Da Kokarin Share Hujja a Kan Zaben Shugaban Kasa

Yanzu Yanzu: PDP Ta Koka, Ta Zargi INEC Da Kokarin Share Hujja a Kan Zaben Shugaban Kasa

  • Jam'iyyar PDP ta zargi INEC da yunkurin lalata hujjar da ke kunshe a na'urorin BVAS da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa na 2023
  • Kakakin jam'iyyar, Debo Ologunagba, ne ya yi zargin yayin wata zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Talata, 7 ga watan Maris
  • Ku tuna cewa INEC ta shigar da bukata na neman a bata izinin sake saita na'urorin BVAS gabannin zaben gwamnoni

Abuja - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da kulla-kulla don lalata hujjar da ke kunshe a na'urorin BVAS da sunan sake saita su.

Debo Ologunagba, kakakin jam'iyyar ta PDP shine ya yi zargin a wani taron manema labarai a Abuja, a daren ranar Talata, 7 ga watan Maris, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

“Duk Bayanan Kan BVAS Na Nan Daidai”: INEC Ta Ba Yan Najeriya Da Kotu Tabbaci

Atiku yana kada kuri'arsa a zabe
Yanzu Yanzu: PDP Ta Koka, Ta Zargi INEC Da Kokarin Share Hujja a Kan Zaben Shugaban Kasa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya ce an shirya taron manema labaran ne don "ankarar da yan Najeriya da kasashen duniya game da wannan danyen aiki da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ke shirin yi na lalatawa tare da goge hujjar magudin da ta yi a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu."

Kakakin PDPn ya kara da cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A daren jiya da misalin 10:10pm, INEC a kokarinta na son hana jam'iyyarmu da dan takararmu samun hujjar da ya kamata kamar yadda kotu ta yi umurni, ta shigar da wata bukata cewa a bari ta sake saita na'urorin BVAS da kuma goge muhimman bayanai da jam'iyyarmu da dan takararmu suka bukata don gabatar da shari'armu a gaban kotun zaben shugaban kasa.
"Wannan mataki da INEC ta dauka na son kawo karan tsaye ga muradin yan Najeriya na neman gyara ta hanyar kotu ya nuna karara hukumar na son haddasa rikici da kuma son kawo cikas ga damokradiyya da son jefa kasar cikin rikici."

Kara karanta wannan

Shin Kwankwaso Ya Taya Zababben Shugaban Kasa Bola Tinubu Murna, NNPP Ta Yi Karin Haske

Mista Ologunagba ya ce idan har hukumar zaben bata da abun da take son boyewa, menene dalilin da zai sa ta nemi a bari ta sake saita na'urorin, rahoton Premium Times.

Ya kuma zargi shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, da jagorantar magudin da aka yi a sakamakon zaben shugaban kasar.

Ologunagba ya ce shugaban na INEC ya gaggauta sanar da wanda ya lashe zaben duk da kokawa da korafe-korafen da aka yi cewa INEC da jami'anta sun yi rashin adalci da keta tanade-tanaden dokar zaben 2022 da dama.

Kotun zabe za ta fara sauraron korafe-korafe

A gefe guda, mun ji cewa kotun zabe za ta fara sauraron koke-koke daga yan takarar shugaban kasa na zaben 2023 da aka kammala da kuma hukumar zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng