Mako 1 da Zabe, Gwamnan PDP Ya Fadi Abin da Ya sa Atiku Ya Rasa Kujerar Shugaban Kasa
- Nyesom Wike yana ganin watsi da Gwamnonin PDP ya jawo Atiku ya sha kasa a hannun Bola Tinubu
- Da ya ziyarci yankin Chokocho-Igbodo, Gwamnan ya maidawa ‘Yan PDP da ke zanga-zanga martani
- Wike ya ce yana cikin wadanda suka dage dole sai mulki ya koma hannun ‘Dan Kudancin Najeriya
Rivers - Gwamna Nyesom Wike ya caccaki Atiku Abubakar da ya jagoranci ‘ya ‘yansu na jam’iyyar PDP zuwa wani zanga-zanga yau a garin Abuja.
Da yake kaddamar da titin Chokocho-Igbodo a karamar hukumar Etche da ke jihar Ribas, Channels TV ta rahoto Nyesom Wike yana zolayar jam’iyyarsa.
Gwamnan na jihar Ribas yake cewa ya gargadi PDP a kan yadda aka nace cewa dole mutanen Arewa za su rike tikitin takara da shugabancin jam’iyya.
Mai girma Wike yake cewa a lokacin da wasu suke yawon zanga-zanga, shi yana kaddamar da ayyukan da ya yi ne domin farantawa al’ummarsa rai.
Nyesom Wike ya yabi
Tashar talabijin ta rahoto Gwamnan yana mai yabawa mutanen jihar Ribas da suka zabi mutumin yankin Kudancin Najeriya ya zama shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya fake da sashe na 7(3)(c) na kundin tsarin jam’iyyar PDP, ya ce ya goyi bayan a rika zagaya da kujeru da mukamai tsakanin bangarorin kasar nan.
Sun ta ce Gwamna Wike yana da ra’ayin cewa PDP ta rasa zaben shugaban kasa ne saboda Atiku Abubakar ya yi watsi da gargadin da G5 tayi masa.
Wike yake cewa da ‘dan takaran ya saurari jan-kunnen da Gwamnonin nan biyar da kungiyar G5 suka yi masa na neman adalci, da labarin ya canza.
Wike: "Burinmu Kudu ta samu mulki"
Fitaccen ‘dan siyasar yake cewa bai da matsala da wadanda suka zabi APC ko LP da suka tsaida ‘dan takaransu daga Kudu, The Nation ta rahoto haka.
"Abin da muke fada a kai kenan, saboda haka dole mulki ya koma Kudu na tawon shekaru takwas domin shugabanci ya shekara takwas a Arewa.
Saboda haka ban zo nan domin hukunta kowa ba. Iyakar sani na, abin da muka hadu a kai shi ne dole sabon shugaban Najeriya ya zama ‘Dan Kudu."
- Nyesom Wike
'Ya 'yan manya a zaben 2023
Ku na da labari yaron Gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai ya kawo karshen Samaila Suleiman a 2023, amma Abba Ganduje ba zai tafi Majalisar tarayya ba.
Mai dakin Ministan harkoki na musamman ta yi nasara a kan ‘Dan majalisar PDP a Benuwai, a jihar Neja kuwa yaron Jerry Gana ya lashe zaben majalisa.
Asali: Legit.ng