‘Dan Shekara 27 Daga Arewa Ya Ajiye Tarihin Zama ‘Dan Autan ‘Yan Majalisar Tarayya
- Ibrahim Bello Mohammed yana cikin zababbun ‘yan majalisar wakilan tarayya a 2023
- Matashin zai zama ‘dan autan ‘yan majalisa a Najeriya yana da shekaru 27 a Duniya
- Kafin IBM, Gabriel Saleh Zock yana cikin masu kananan shekarun da suke majalisa
Abuja - Ibrahim Bello Mohammed wanda aka fi sani da IBM ya shiga littafin tarihi bayan nasarar da ya samu a zaben majalisar wakilan tarayya.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Alhaji Ibrahim Bello Mohammed ya lashe kujerar ‘dan majalisar mazabun Birnin-Kebbi, Kalgo da kuma Bunza.
Baturen zaben majalisar wakilan tarayya a yankin, Abbas Aliyu Bazata ya tabbatar da Ibrahim Mohammed a matsayin wanda ya samu nasara.
Da yake sanar da sakamakon zaben, Abbas Bazata ya ce jam’iyyar adawa ta PDP tayi nasara da kuri’u 50,781 a kan ‘dan takaran APC mai 37,478.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton ya ce Jam’iyyar hamayya ta SDP ta zo ta uku a zaben da kuri’u 7,880 a zaben da aka yi.
Wakilcin Ibrahim Bello Mohammed
Da yake jawabi a makon jiya, Ibrahim Bello Mohammed ya godewa mutanen Birnin Kebbi da kewaye da suka zabe shi domin ya wakilce su.
Matashin mai shekara 27 da haihuwa ya sha alwashin zai iya amfani da kuruciyarsa wajen kawowa mutanen mazabarsa cigaba a majalisar tarayya.
Intel ta ce kafin yanzu, Gabriel Saleh Zock da ya tafi majalisa a karkashin jam’iyyar APC ne ‘dan siyasa mai mafi karancin shekaru da ya je majalisa.
Gabriel Saleh Zock mai wakiltar Kachia/Kagarko na jihar Kaduna yana da shekaru kusan 38.
'Dan gidan na-gada ba na-koya ba
Ba a banza matashin ya lashe zabe da ratar fiye da kuri’u 13, 000 ba, mahaifinsa ya taba zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa a farkon 2011.
Baya ga haka, a 2015 Dr. Bello Halliru Muhammad ya zama shugaban majalisar amintattu na jam’iyyar bayan tafiyar Cif Anthony Anenih.
Nasarar Abdulhakeem Kamilu Ado
Kwanaki an ji labari Sheikh Abdulhakeem Kamilu Ado Wudil wanda mahaddacin Qur'ani, makarancin Hadisi ne zai zama ‘Dan Majalisa a NNPP.
Abdulhakeem Kamilu Ado Wudil ya canji mahaifinsa da ya rasu daf da zabe. Zababben 'dan majalisar yana da shekara 30 ne a Duniya.
Asali: Legit.ng