Ainihin Dalilan da Suka Jawo APC Ta Ji Kunya a Legas, Kaduna, Katsina da Jihohi 9
- Bola Tinubu ya fadi wasu jihohin da ba ayi tunani ba a zaben shugaban kasa da aka yi a kwanaki
- Jam’iyyun PDP, NNPP da LP sun yi nasara a Jihohin Kano, Kaduna, Filato, Yobe da APC ta ke da karfi
- Ana ganin akwai laifin tsare-tsaren Gwamnatin El-Rufai, canza kudi, rikicin cikin gida da guguwar LP
Abuja - Zaben shugaban kasa da aka yi wannan karo ya zo da abubuwan mamaki, daga ciki akwai nasarar da jam’iyyar adawa ta LP ta samu a Legas.
A wani dogon rahoto, Daily Trust ta bi diddigin abin da ya jawo APC da ‘dan takaranta, Bola Tinubu suka sha kashi a wasu daga jihohin Najeriya.
Matasan da ke yi wa kansu lakabi da ‘Obidient’ suka jawo Bola Tinubu ya ji kunya a Legas, Kiristocin Yarbawa da Ibo sun goyi bayan LP a kan APC.
Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa rikicin cikin gidan da aka gagara shawo kan shi ne ya jawo APC ta gagara samun nasara a jihar Kuros Ribas.
Matsalolin Katsina, Kaduna, dsr
A jihar Katsina, matsin tattalin arziki, tsarin canza kudi da wahalar rayuwa tare da cin amana ya taimakawa PDP wajen nasarar da ta samu a kan APC.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sabani da makarkashiyan wasu ‘yan jam’iyya ya yi sanadiyyar da APC ta rasa jihar Nasarawa, ana zargin ‘yan cikin gida sun ci amanar Gwamna A. A Sule.
Masu nazarin siyasa su na gamin hakan bai rasa nasaba da tsare-tsaren CBN da Gwamnatin El-Rufai na rusa gidaje, korar ma’aikata da kara kudin karatu.
A Filato kuwa addini ya yi amfani wajen doke APC da LP tayi a zaben shugaban kasa. Sannan samun takarar Nentawe Yilwadta ya fusata wasu ‘Yan APC.
Tun 1999 PDP ta ke mulki a Ebonyi sai da Gwamna David Umahi ya koma APC a 2020. Karbe jihar da APC tayi ya ba LP damar samun kuri’u a zaben bana.
A Kano kuwa, takarar Rabiu Musa Kwankwaso a NNPP ta hana APC kai labari.
Wasu masana su na ganin Gwamnonin da ba su neman tazarce ba su tallata ‘yan takaran majalisa ba, sun fi maida hankali a yakin zaben Bola Tinubu.
PDP za tayi zanga-zanga
A yau aka ji Shugabannin PDP za su soma zanga-zanga a Abuja domin nunawa INEC fushinsu a kan rashin nasarar Atiku Abubakar a zaben 2023.
Kwamitin neman takara ya rabu da ‘Yan G5 wajen zanga-zangar. Dr Iyorchia Ayu da Dr. Ifeanyi Okowa za su jagoranci zanga-zanga da bakaken kaya.
Asali: Legit.ng