“Kanzon Kurege Ne”: PDP Reshen Osun Ta Yi Martani Kan Rade-radin Sauya Shekar Gwamna Adeleke
- Jam'iyyar PDP ta ce Gwamna Ademola Adeleke baya da niyan barin jam'iyyar zuwa APC
- Jam'iyyar reshen jihar Osun ta bayyana hakan ne yayin martaninta ga rade-radin sauya shekar Adeleke a soshiyal midiya
- PDP ta bukaci jama'a da su yi watsi da rade-radin sauya shekar, wacce ta bayyana a matsayin kanzon kurege
Osun - An yi watsi da rade-radin sauya shekar Gwamna Ademola Adeleke daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jam'iyyar PDP reshen jihar Osun ta bayyana rade-radin da ake yadawa a soshiyal midiya a matsayin kanzon kurege, jaridar Vanguard ta rahoto.
A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban rikon kwarya, Dr Akindele, ya ceAPC ce ta kagi jita-jitan.
Sanarwar ta ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ina mai bukatar jama'a da su yi watsi da rade-radin sauya shekar. Babu dalilin haka, musamman duba ga nasarar da ya jagoranci PDP a kai yan kwanaki da suka gabata a zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin tarayya a jihar Osun.
"An yi wa APC reshen Osun mummunan illa kuma tana fafutukar neman tashi a kafarta."
Ku zabi PDP a ranar 11 ga watan Maris, PDP ga mutanen Osun
Akindele ya kira rahoton a matsayin ajandar dauke hankali mara tasiri, yayin da ya bukaci masu zabe a jihar Osun da su fito kwansu da kwarkwata sannan su zabi yan takarar PDP a zabe mai zuwa a ranar 11 ga watan Maris, rahoton Channels TV.
Ya nuna yakinin cewa PDP za ta lashe kujerun yan majalisar jiha 26 a zaben ranar 11 ga watan Maris.
Shugaban rikon kwaryan ya kara da cewar Adeleke ya nuna cewa shugabanci nagari na iya yiwuwa cikin kwanaki 100, yana mai cewa gwamnan jihar Osun yana nan tare da PDP.
Ya yi kira ga masu zabe da su yi watsi da karairayin cewa:
"Gwamna Adeleke na nan a matsayin jigo kuma gwamnan PDP."
Ku yarda da sakamakon zabe, Allah ke bayar da mulki, Sultan ga yan Najeriya
A wani labarin, sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Abubakar Sa'ad ya bukaci al'ummar Najeriya da su yi biyayya ga shugabanninsu don Allah ke bayar da mulki.
Asali: Legit.ng