Tsakanin Atiku da Obi, Akwai Mai Karyar Shi Ya Lashe Zabe – Tsohon Shugaban APC
- Atiku Abubakar da Peter Obi duk ba su yarda da sakamakon zaben 2023 ba, su na ganin APC tayi magudi
- Kowane ‘Dan takaran ya ce shi ne asalin wanda ya yi galaba, ba Bola Tinubu na Jam’iyya mai-mulki ba
- Sanata mai jiran-gado, Oshiomhole yana ganin ba za ta yiwu a ce dukkaninsu biyu sun yi gaskiya ba
Edo - Kwamred Adams Oshiomhole wanda ya taba zama shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya maida raddi ga Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi.
‘Yan takaran shugabancin kasar na jam’iyyun hamayya su na kalubalantar nasarar APC, Vanguard ta ce Adams Oshiomhole ya yi masu raddi.
Zababben Sanatan na Edo ta Arewa ya ce a cikin Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar da Peter Obi, lallai akwai wanda yake yi wa jama’a karya.
Bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, Atiku da Obi duk sun fito su na ikirarin an yi magudi, kowa yana cewa shi ne ya lashe zabe.
Jawabin Adams Oshiomhole
An rahoto Kwamred Oshiomhole yana mai cewa babu yadda za ayi ya zama dukkansu su na fadan gaskiya game da zaben da aka shirya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsakanin Mai girma Peter Obi da babban abokina, Mai girma Atiku Abubakar, dole wani daga cikinsu karya yake yi.
Domin kuwa Atiku wanda ya zo na biyu ya ce ya lashe zaben, Obi wanda ya zo na uku, ya ce a’a, shi ne ya samu nasara.
Saboda haka a tsakaninsu, dole su na kokarin yi wa junansu magudi, don haka wani daga cikin karya yake shararawa.
Idan suka je kotu, na tabbata za a nuna cewa idan mutane biyu suna ikirarin nasara, su na cewa sun yi wa juna magudi ne.
- Adams Oshiomhole
Oshiomhole ya ce yi zaben gaskiya da adalci
Daily Post a rahoton da ta fitar, ta ce tsohon Gwamnan na jihar Edo yana ganin ko a wajen zuwa na biyu a takarar, PDP da LP sun yi juna murdiya.
Jagoran jam’iyyar mai-mulki ya yabi ‘yan takaran saboda ganin yadda suka bi doka, ya ce rasa Legas da APC tayi, ya nuna an yi zaben gaskiya.
Jihohi 6 su na kotu
Jihohin Adamawa, Akwa-Ibom, Bayelsa, Delta, Edo da Sokoto ba su gamsu da zaben 2023 ba. An ji labari Jihohin nan 6 na zargin INEC ta saba doka.
Mike Ozekhome wanda ya shigar da kara a madadin gwamnatocin jihohin ya sanar kotun koli an ki aika sakamakon zaben ta na’urorin lantarki.
Asali: Legit.ng