"Ku Yi Duk Mai Yiwuwa Wajen Kare Ƙuri'un Ku" Jam'iyyar PDP Ta Sokoto Ga Mambobinta

"Ku Yi Duk Mai Yiwuwa Wajen Kare Ƙuri'un Ku" Jam'iyyar PDP Ta Sokoto Ga Mambobinta

  • A yayin da ake dab da ayi zaɓen gwamnoni a Najeriya, jam'iyyar PDP a jihar Sokoto, tayi wani muhimmin kira ga mambobin ta
  • Jam'iyyar ta nemi mambobin ta da su tabbatar sun fito ƙwansu da ƙwarƙwartar su sun yi zaɓe
  • Ta kuma buƙace su da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun tsare abinda suka zaɓa a ranar zaɓen

Sokoto- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), reshen jihar Sokoto ta yi kira ga mambobin ta kan suyi duk mai yiwuwa wajen ganin sun kare ƙuri'un su a lokacin zaɓen gwamnan jihar.

Jam'iyyar tayi wannan kiran ne a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis. Rahoton Daily Trust

Jam'iyyar ta gudanar da taro ne domin samu hanyoyin da zata lashe zaɓukan da basu kammalu ba na ƴan majalisun tarayya a jihar. Rahoton Gazettengr

Kara karanta wannan

Shugaban APC Na Ƙasa Ya Caccaki PDP Da LP, Ya Tono Wata Maƙarƙashiyar Da Suke Ƙullawa

Jam'iyyar PDP
"Ku Yi Duk Mai Yiwuwa Wajen Kare Ƙuri'un Ku" Jam'iyyar PDP Ta Sokoto Ga Mambobin Ta Hoto: The Cable
Asali: UGC

Da yake jawabi ga mambobin jam!iyyar, Bello Goronyo, shugaban jam'iyyar na jihar, ya ce ba su da wani ƙwarin guiwa akan jami'an tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina son da ku fito ku kaɗa ƙuri'un ku a lokacin zaɓe sannan kun yi zaɓe ku tsaya ku kare kuri'un ku."
"Ku yi duk abinda za ku iya yi domin kare ƙuri'un ku. Idan wani ya zage ku, ku rama. Idan wani ya buge ku, ku rama kuma." A cewar sa

Sai dai, a na shi jawabin, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya buƙaci mambobin jam'iyyar da su cafke duk wani wanda ya nemi ya kawo hargitsi a lokacin zaɓen.

“Ina goyon bayan matsayar jam'iyyar mu. Ina son da ku fito ku kaɗa ƙuri'un ku. Bayan kun yi zaɓe, ku tsaya ku tsare ƙuri'un ku. Ku tabbatar kun tsare har zuwa wajen tattara sakamakon zaɓe."

Kara karanta wannan

Mun gano INEC Na Ƙirƙirar Ƙuri'un Shafcin Gizo-da-Koƙi - Shugaban Labor Party

“Idan wani yazo tayar da hargitsi, ku kama shi ku ɗaure har sai an kammala zaɓe." A cewar sa

Jam'iyyar PDP Ta Yi Watsi Da Nasarar Tinubu, Ta Ce Atiku Ne Ya Ci Zabe

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar PDP tayi watsi da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, tace Atiku Abubakar ne ya lashe zaɓe.

Hukumar INEC dai ta sanar da ɗan takarar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng