Kabilanci da Abubuwa 6 da Suka Yi Tasiri a Zaben Sabon Shugaban Kasa da Majalisa
- Cibiyar CDD mai kula da harkar cigaban damukaradiyya tayi aiki a kan babban zaben Najeriya
- Ma’aikatan cibiyar sun sa ido a zabukan da aka shirya a fadin jihohin kasar 36 da birnin Abuja
- Darektar CDD, Idayat Hassan ta jero abubuwan da suka yi tasiri a zaben shugabannin kasar
Daily Trust ta rahoto bayanan da cibiyar CDD ta wallafa a game da zaben na bana:
1. Dabi’ar masu zabe
Binciken CDD ya nuna an yi amfani da kabilanci wajen zaben mai takara. Matasan Ibo da Arewa ta gabas sun rika zaben wanda ya fito daga yankinsu.
2. Jama’a ba su fita ba
A cikin wadanda suka tanadi katin PVC, 35% na mutanen ne kurum suka fita domin kada kuri’a, an samu raguwar masu zabe a karon farko tun 2003.
3. Sayen kuri’u
Sannan an fahimci an samu sauki wajen sayen kuri’u, musamman idan aka kamanta da abin da ya faru a lokacin zaben Gwamnan jihar Osun na 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
4. Barazana
3.4% na masu lura da zabe sun tabbatar da an samu tashin-tashina ko yunkurin yi wa masu zabe barazana, ‘yan dabar sun yi haka a irinsu Legas.
5. Mace-mace
Baya ga hana mutane kada kuri’arsu, an rahoto mutuwar mutane 10 a sanadiyyar abin da ya shafi zabe a Jihohin Abia, Ribas, Kano, Ondo, Kogi da Delta.
6. Barnata kayan zabe
Rahoton ya nuna duk da ba a samu barkewar rigima sosai ba, an lalata kayan zabe a rumfuna kusan 2000 a zaben nan, wannan ya shafi 1.2% na masu zabe.
7. Jita-jita
Legit.ng Hausa ta fahimci an rika yada karya cewa Peter Obi ya janyewa Atiku Abubakar ko ‘yan PDP su na kitsa yadda za a murde zaben da za ayi.
Gwamnatin hadaka a 2023?
An ji labari tsohon Gwamnan Ekiti, Kayode John Fayemi ya fadi abin da ya kamata Gwamnatin Tinubu ya yi wa su Rabiu Kwankwaso da su Peter Obi.
Idan ya dare kujerar shugaban Najeriya, Fayemi yana so a jawo ‘yan adawa. Bola Tinubu ya nuna alamar zai gayyaci abokan gabarsa su yi aiki tare.
Asali: Legit.ng