Shugaban Kasa: Tinubu Zai Karbi Satifiket Din Cin Zabe Da Karfe 3 Na Ranar Laraba

Shugaban Kasa: Tinubu Zai Karbi Satifiket Din Cin Zabe Da Karfe 3 Na Ranar Laraba

  • Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, Farfesa Yakubu Mahmood ya bayyana lokacin da INEC za ta bayar da satifiket din cin zabe
  • Hukumar INEC ta ce za ta bai wa Bola Tinubu, zababben shugaban kasa takardar shaidar cin zabensa da karfe 3:00 na ranar Laraba, 1 ga watan Maris
  • Mahmood ya ce za a sanar da ranar da zababbun sanatoci da yan majalisar wakilai za su samu nasu satifiket din

Abuja - An ayyana Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shugaban kasa na 2023, a matsayin wanda ya lashe zabe.

Bayan ya samu kuri'u mafi rinjaye da ya kai 8,794726, an bayyana tsohon gwamnan na jihar Lagas a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Ku rungumi kaddara: Tinubu ya tura sako mai daukar hankali ga Atiku da Peter Obi

Zababben shugaban kasar Najeriya
Shugaban Kasa: Tinubu Zai Karbi Satifiket Din Cin Zabe Da Karfe 3 Na Ranar Laraba Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Yaushe Tinubu zai karbi satifiket din cin zabe

Bayan ayyana shi, shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da cewar zababben shugaban kasar zai karbi satifiket din cin zabe da misalin karfe 3:00 na ranar Laraba, 1 ga watan Maris.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yakubu ya yi sanarwar ne bayan ayyana dan takarar na APC a matsayin zakaran gwajin dafin zaben a safiyar ranar Laraba, kamar yadda jaridar Legi.ng ta sanya idanu.

Jaridar Aminiya ta nakalto Mahmood yana cewa:

“A yau da misalin karfe 3:00 na rana hukumar zabe za ta ba wanda ya ci zabe takardar shaidar cin zabe.
“Daga baya hukumar zabe za ta sanar da lokacin da wadanda suka lashe zaben yan Majalisar Wakilai da Sanatoci za su samu satifiket din shaidar cin zabensu."

Kara karanta wannan

Za a Sake Zabe:, INEC Ta Ayyana Zaben Zamfara Ta Tsakiya a Matsayin Ba Kamalalle Ba

Shugaban Izala ya yi kakkausar gargadi ga yan siyasa a fadin Najeriya

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau, ya ja hankalin yan siyasa a bangarori daban-daban na kasar da su guji furta kalamai masu hatsari wadanda ka iya kawo hargitsi ga aikin zaben da hukumar INEC ke yi.

Sheikh Bala Lau ya bukaci duk dan siyasar da bai gamsu ba ko yake ganin ba a yi masa adalci ba a zaben da ya bi tsarin doka ta damokradiyya wajen neman hakkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng