Sakamakon Zabe: Atiku Abubakar Ya Samu Nasara a Jihar Taraba

Sakamakon Zabe: Atiku Abubakar Ya Samu Nasara a Jihar Taraba

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya tumurmusa abokan hamayyarsa ya lashe zabe a jihar Taraba
  • A sakamakon da INEC ta sanar a matakin jiha, jam'iyyar PDP ce kan gaba da kuri'u mafiya rinjaye yayin da Labour Party ta zo na biyu
  • Jam'iyyar APC da Bola Tinubu ke neman zama shugaban kasa ta mara masu baya a matsayi na uku, NNPP a matsayi na hudu

Taraba - Alhaji Atiku Abubakar, mai neman zama shugaban kasa a inuwar Peoples Democratic Party (PDP) ya lashe zaben da ya gudana ranar Asabar a jihar Taraba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Atiku ya lallasa takwaransa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na jam'iyyar APC mai mulki.

Alhaji Atiku Abubakar.
Atiku na jawabi. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: UGC

Baturen zaben jihar wanda INEC ta ɗora wa Alhakin tattara sakamakon, Farfesa Mohammed Abdulazeez, na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ne ya sanar da haka.

Kara karanta wannan

Zaben Shugaban Kasa: Peter Obi Ya Lallasa Atiku Da Tinubu a Jihar Cross River

A cewarsa, jam'iyyar PDP ta lashe kuri'u 189,017 wanda suka ba ta damar lallasa Labour Party, wacce ta zo na biyu da kuri'u 146,315.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka nan jam'iyyar APC ta tashi da kuri'u 135,165 yayin da jam'iyyar New Nigeria Peoples Party watau NNPP mai kayan marmari ta zo na huɗu da kuri'u 12,818.

Legit.ng Hausa ta tattaro yadda sakamakon ya fito da adadin kuri'un da kowace jam'iyya ta samu, ga su kamar haka;

PDP - 189,017

LP - 146,315

APC - 135,165

NNPP - 12,818

APGA – 4526

SDP – 4000

PRP – 579

A halin yanzun jihar Taraba ta shiga jerin jihohin da tsohon matainakin shugaban kasan ya samu galaba. INEC ta ƙasa na ci gaba da tattara sakamako daga jihohi a Abuja.

A ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, 'yan Najeriya suka nufi rumfunan zabe a sassan ƙasar domin zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya, kamar yadda Premium Times ta tattaro.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu, Obi Atiku? INEC Ta Fadi Wanda Ya Lashe Zabe a Kogi

Okowa ya gaza kawo jiharsa ga PDP

A wani labarin kuma Peter Obi Ya Lallasa PDP a Jihar Abokin Takarar Atiku Abubakar, gwamna Okowa

A sakamakon da jami'in INEC ya sanar yau Talata, ya ce jam'iyyar Labour Party na gaban PDP da APC da kuri'u masu rinjaye a zaben da ya gudana Asabar ɗin da ta shige.

Asali: Legit.ng

Online view pixel