Cibiyoyin Amurka Sun Jero Wuraren da Aka Samu Matsala a Zaben Shugaban Najeriya
Cibiyoyin bincike da nazari na Duniya na IRI da NDI sun yi nazarin zabukan da aka shirya a Najeriya
IRI, IEOM, NDI su na ganin kyawu, inganci da nagartar zaben bai kai yadda al’umma suka sa rai ba
Wadannan kungiyoyi sun ce shirun da INEC tayi wajen tattara kuri’u ya jawo alamar tambaya
Abuja - Cibiyar IRI ta kasashen Duniya da takwararta, cibiyar NDI da kungiyar IEOM ta masu lura da harkar zabe, sun soki zaben da aka yi a fadin Najeriya.
Tribune ta kawo rahoto a ranar Talata cewa cibiyoyi da kungiyoyin nan sun ce duk da gyare-gyaren da aka kawo, zaben 2023 bai yi kyawun da ake sa rai ba.
Kungiyar hadakar sa-ido da tsohon shugaban kasar Malawi, Dr. Joyce Banda ya jagoranta tace an samu kalubale wajen kai kayan aiki zuwa wuraren zabe.
Joyce Banda ya ce rigingimu da suka barke a wasu wurare sun bata nagartar zaben na bana.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Banda ya ce mutane sun jajirce
"Duk da yawan jama’a a wasu rumfunan yin zabe da kuma dogon jira da aka yi, masu zabe a Najeriya sun nuna jajircewa da ganin kuri’arsu tayi tasiri.
Mu na taya mutanen Najeriya murna saboda tsayawa tsayin-dakarsu na ganin sun shiga zaben."
NDI/IRI sun aika mutane 40 zuwa kowane yanki da yake kasar nan domin ganin yadda mutane su ke kada kuri’a a zaben sabon shugaban kasar Najeriya.
Matsalolin da aka samu a 2023
Bayanan da kungiyoyin nan suka bada ya tattaro wasu aubuwan da aka gano a zaben, tare da bata shawarwarin yadda za a magance su a zabe na gaba.
"A karshen zaben, an samu kalubale wajen aika sakamako ta na’ura domin a wallafasu saboda kowa ya rika gani a lokacin da ya kamata, wanda hakan ya taba ingancin zaben a mafi muhimmancin lokaci.
Baya ga haka, rashin bayani da fitowa karara na hukumar INEC ya kara jawo rudani, kuma ya rage yawan masu zabe a yanayin.
Duk da wadannan matsaloli, ‘Yan Najeriya sun nuna da gaske wajen ganin sun bada gudumuwarsu a harkar damukaradiyya.
A karshe an yi kira ga jama’a musamman masu ruwa da tsaki, su kwantar da hankalinsu yayin da ake tattara kuri’a, ana neman hadin-kan al’umma
Sakon Sanata Hadi Sirika
Rahoto ya zo cewa Sanata Hadi Sirika ya fito shafinsa na Twitter yana nuna Asiwaju Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa da aka shirya a ranar Asabar.
Ministan ya fadawa wakilan Atiku Abubakar abin da ya dace su yi idan ba su gamsu da sakamakon ba, a maimakon su yi abin da zai nuna rashin kishi.
Asali: Legit.ng