Tinubu Ya Lashe Zabe a Karamar Hukumar Gwamna Wike da Tazara Mai Yawa
- Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya tabbatar da kalamansa na kai Atiku ƙasa a zaben yankinsa
- Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na APC ne ya samu nasara a karamar hukumar Wike
- Gwamnan Ribas ya samu sabani da Atiku tun bayan kammala zaben fidda gwanin PDP a watan Mayun bara
Rivers - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar All Progressive Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya samu nasara a karamar hukumar Obio-Akpor da ke jihar Ribas.
Daily Trust ta ce Tinubu ya samu nasara da tazara mai ɗumbin yawa zaben a shugaban kasan da ya gudana a Obio-Akpor, yankin da gwamna Nyesom Wike na Ribas ya fito.
Sakamakon ya nuna cewa Tinubu ya lashe kuri'u 80, 239 inda ya lallasa abokin karawarsa Peter Obi, wanda ya zo na biyu da tazara mai nisa, ya samu kuri'u 3,829.
Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya samu saɓani da gwamna Wike, ya samu kuri'u 368, kamqr yadda The Nation ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai wakilan jam'iyyar Labour Party sun fusata da jin sakamakon tun a zauren tattara wa inda suka zargi jami'an hukumar zaɓe INEC da damfarar zaɓe.
Bayan sun ɗaga murya tare da yin Allah wadai da sakamkon zsben, wakilan LP guda biyu sun lashi takobin cewa ba zasu taɓa aminta da sakamakon ba.
Baturen zaben jihar Ribas, mai alhakin tattara sakamako, Farfesa Teddy Adias, ya ba su shawarin su kai korafinsu zuwa wurin da ya dace kuma su bi matakai.
Gwamnan Wike na ɗaya daga cikin gwamnonin G-5 na jam'iyyar PDP, waɗanda suka fusata kuma suka ja daga da shugabancin jam'iyya na ƙasa karkashin Iyorchia Ayu.
Tun da fari, tawagar gwamnonin da sauran jiga-jigan da ke mara masu baya suka tsame hannunsu daga cikin kwamishin kamfen Atiku Abubakar.
Atiku ya samu nasara a Taraba
A wani labarin kuma Fafatawa Ta Yi Zafi, Atiku Abubakar Ya Samu Nasara a Jihar Taraba
Waizirin Adamawa ya lallasa manyan abokan hamayyarsa a sakamakon zaben shugaban kasan da INEC ta bayyana a jihar Taraba.
Asali: Legit.ng