Yanzu Yanzu: “Ba Zan Sauka Ba”: Shugaban INEC Ya Mayar Da Martani Ga Atiku, Obi

Yanzu Yanzu: “Ba Zan Sauka Ba”: Shugaban INEC Ya Mayar Da Martani Ga Atiku, Obi

  • Daga karshe shugaban hukumar zabe, Farfesa Mahmood Yakubu ya mayar da martani ga masu neman ya yi murabus
  • Farfesa Mahmood ya ce ba zai sauka daga kujerarsa ba domin yin hakan baya bisa ka'ida
  • Shugaban na INEC ya ce duk wanda bai gamsu da sakamakon zabe ba ya jira a kammala sai ya tunkari kotu da hujjojinsa

Abuja - Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce kira da jam'iyyun Labour Party (LP) da na People’s Democratic Democratic Party (PDP) suka yi na neman ya yi murabus bai dace ba.

Wasu jam'iyyu sun bayyana cewa sun rasa karfin gwiwa kan tsarin zaben da ke gudana saboda rashin amfani da na'urar aika sakamako kamar yadda dokar zabe ta tanada.

Shugaban INEC a cibiyar tattara sakamako na kasa
Yanzu Yanzu: “Ba Zan Sauka Ba”: Shugaban INEC Ya Mayar Da Martani Ga Atiku, Obi Hoto: INEC
Asali: Twitter

A wani jawabi da suka yi a Abuja, jam'iyyun adawa sun yi zargin magudi a zaben da aka yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zabe: An Yi Wa Atiku Kayen Raba Ni da Yaro a Jihar Abokin Takararsa Okowa

Jaridar Punch ta rahoto cewa jam’iyyun Peoples Democratic Party, Labour Party da African Democratic Congress sun bukaci shugaban INEC ya yi murabus.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai da yake martani ta hannun Rotimi Oyekanmi, babban sakataren labaransa, shugaban INEC ya ce sabanin hasashen da jam'iyyun biyu ke yi, sakamakon zaben da ke fitowa daga jihohi na gaskiya ne kuma sahihai ne.

Duk wanda bai gamsu ba ya jira a gama zabe sai ya tunkari kotu, INEC

Hukumar ta kuma ce zargin da Sanata Dino Melaye ya yi cewa shugaban INEC ne ke baiwa jam'iyyu maki ba gaskiya bane kuma bai kamata ba, rahoton Daily Trust.

"Don tabbatar da haka, fusatattun jam'iyyu na da yancin zuwa kotuna don bayyana damuwarsu sannan su jira a warware lamarin. Yin kalaman da ka iya haddasa rikici da tashin hankali ba abun yarda bane.

Kara karanta wannan

"A Soke Wannan Zaben Ayi Sabon Lale" Kwamitin Kamfen Atiku Ya Yi Kira Ga INEC

"Tsare-tsare babban zaben 2023 suna matakan karshe na kammaluwa. Zai kamata ne kawai jam'iyyun su bari a kammala tsarin sannan su tunkari kotu da hujjojinsu don yin shari'a.
"Akwai shiryayyun ka'idoji da fusatattun jam'iyyu ko yan takara za su bi idan basu gamsu da sakamakon zabe ba. Wadannan matakan basu hada da neman shugaban INEC ya yi murabus ko a soke zabe ba."

Zaben shugaban kasa: Tinubu ya lallasa Atiku da Obi a Kogi

A wani labarin, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya lallasa manyan abokan hamayyarsa a jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng