Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Lashe Zabe a Jihar Oyo, Ya Lashe Gaba Daya Kananan Hukumomi 33
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Oyo kamar yadda INEC ta sanar
- Tinubu ya samu kuri'u 449,884 a fadin kananan hukumomi 33 na jihar inda ya yi wa sauran abokan hamayyarsa zarra
- Atiku Abubakar na PDP ya zo na biyu da kuri'u 182,977, Peter Obi na da 99,110 yayin da Sanata Rabiu Kwankwaso na NNPP ke da 4095
Oyo - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar a jihar Oyo kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta sanar.
Tinubu ya lashe zabe a kananan hukumomi 33 na jihar yayin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya zo na biyu, jaridar Punch ta rahoto.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi,, ya zo na uku a zaben da aka gudanar a fadin jihar.
Yawan kuri'un da kowani dan takara ya samu
Kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto, Tinubu ya samu jimilar kuri'u 449,884, Atiku ya samu kuri'u 182,977, Obi ya tashi da 99,110 yayin da Sanata Rabiu Kwankwaso na NNPP ya samu 4095.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Baturen zabe na kananan hukumomin jihar ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zabe, sakatariyar INEC da ke Agodi, Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Litinin, 27 ga watan Fabrairu.
Ga wasu daga cikin sakamakon kananan hukumomin a kasa:
Karamar hukumar Ibadan ta arewa maso yamma
APC 13078
PDP 6011
LP 4820
Karamar hukumar Kajola
APC 11917
PDP 9358
LP 503
Karamar hukumar Afijio
APC 8876
PDP 4112
LP 1925
Karamar hukumar Itesiwaju
APC 6180
PDP 4948
LP 387
Karamar hukumar Atisbo
APC 7928
PDP 4031
LP 1178
Karamar hukumar Atiba
APC 15046
PDP 6180
LP 1234
Karamar hukumar Lagelu
APC 16011
PDP 5112
LP 4066
Karamar hukumar Oyo ta yamma
APC 14076
PDP 4544
LP 1724
Karamar hukumar Iseyin
APC 19731
PDP 6588
LP 1371
Karamar hukumar Ibarapa ta gabas
APC 10575
PDP 4800
LP 779
Karamar hukumar Saki ta gabas
APC 6414
PDP 3634
LP 1144
Karamar hukumar Ibarapa ta tsakiya
APC 10291
PDP 5169
LP 726
A wani labarin, mun kawo cewa Bola Tinubu na gaba da Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a sakamakon kananan hukumomin jihar Sokoto 10.
Asali: Legit.ng