Bayan ta Kunyata Ganduje, NNPP Ta Hana Yaron Gwamna Zuwa Majalisar Tarayya
- Umar Abdullahi Ganduje yana cikin wadanda jam’iyyar NNPP ta dankara da kasa a jihar Kano
- Yaron Gwamnan ya sha kashi a hannun ‘dan majalisarsa, Honarabul Abdulkadir Tijjani Jobe
- Ganduje bai yi nasarar zama ‘dan majalisar tarayya ba, Jobe zai koma majalisa a karo na biyar
Kano - Umar Abdullahi Ganduje wanda aka fi sani da Abba Ganduje, bai yi nasara a yunkurinsa na zama ‘dan majalisar wakilan tarayya ba.
Vanguard ta ce Abba Ganduje ya sha kayi a hannun Honarabul Abdulkadir Tijjani Jobe wanda yanzu shi ne yake rike da wannan kujerar.
Abdulkadir Tijjani Jobe ya lashe zaben mazabar Tofa, Dawakin-Tofa da Rimingado a karo na biyar.
Jobe wanda ya tsaya takara a jam’iyyar hamayya ta NNPP, ya samu kuri’u 52,457, shi kuma Umar Abdullahi Ganduje ya samu 44,809 a APC.
INEC ta sanar da wanda ya ci zabe
Daily Trust ta ya tabbatar da Farfesa Saminu Yahaya ya bada sanarwar sakamakon a babban ofishin INEC na yankin da ke Dawakin Tofa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zuwa yau Abdulkadir Tijjani Jobe ya yi shekaru 20 a majalisar tarayya, shi kuma Abba Ganduje wannan ne karon farko da ya shigo harkar.
Ficewar Jobe daga APC
A dalilin sabani da aka samu tsakanin Jobe da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, sai ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar NNPP a shekarar bara.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa duk da alamun nasarar da NNPP ta samu a jihar Kano, ta rasa wasu kujeru da ke yankin Arewacin Jihar.
Magoya bayan jam’iyyar sun tabbatar da ‘dan takaransu na Sanatan Kano ta Arewa, Abdullahi Baffa Bichi bai iya doke Sanata Barau Jibrin ba.
Akwai yiwuwar APC ta rike kujerar ‘dan majalisar tarayya na yankin Bichi da kuma Kabo/Gwarzo.
NNPP: Maraya ya ci zabe a Kano
Abdulhakeem Kamilu Ado Wudil ya samu kujerar Wudil da Garko a Majalisar Tarayya a Kano a sanadiyyar rasuwar mahaifinsa a makon jiya.
Kamar yadda labari ya zo a yammacin Lahadi, Hon. Kamilu Ado Wudil ya rasu ne a lokacin da ake shirya-shiryen yin zabe, sai yaronsa ya gaje shi.
Asali: Legit.ng