Zaben 2023: Tinubu Na Gaban Obi da Atiku a Ondo Yayin da Sakamakon Zabe Ke Fitowa
- Sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu na ci gaba da fitowa
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC ne a kan gaba a sakamakon kananan hukumomi uku na jihar Ondo da ka sanar zuwa yanzu
- Yankunan da aka sanar zuwa yanzu sun hada da Akure ta arewa, Akoko ta kudu maso gabas da kuma Akoko ta kudu maso yamma
Ondo - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya lashe sakamakon zabe a kananan hukumomin uku na jihar Ondo da aka sanar zuwa yanzu.
Kananan hukumomin sune Akure ta arewa, Akoko ta kudu maso gabas da kuma Akoko ta kudu maso yamma, rahoton Daily Trust.
A Akure ta arewa Tinubu ya samu kuri'u 14,261 wajen lallasa takwarorinsa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, da Labour Party, Peter Obi wadanda suka samu 4,633 da 2,945 kowannensu.
Akoko ta kudu maso gabas, Tinubu ya samu kuri'u 10,765, Atiku 3,016 yayin da Obi ya samu 470.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A Akoko ta kudu maso yamma, Tinubu ya samu kuri'u 28,367, Atiku ya samu kuri'u 5,376 yayin da Obi ya samu 920.
Ga cikakken sakamakon zaben a kasa:
Akure ta arewa
Masu rijista – 79,272
Wadanda aka tantance – 23,917
A: 24
AA: 11
AAC: 35
ADC: 288
ADP: 54
APC: 14,261
APGA: 39
APM: 19
APP: 22
BP: 21
LP: 2,945
NNPP: 66
NRM: 14
PDP: 4,633
PRP: 08
SDP: 48
YPP: 12
ZLP: 374
Jimlar kuri'u masu inganci – 22,874
Lalatattun kuri'u – 1,024
Jimlar zaben da aka kada– 23,898
Akoko ta kudu maso gabas
Masu rijista – 40,592
Wadanda aka tantance – 14,783
A: 00
AA: 00
AAC: 07
ADC: 97
ADP: 37
APC: 10,765
APGA: 13
APM: 03
APP: 03
BP: 00
LP: 470
NNPP: 07
NRM: 08
PDP: 3,016
PRP: 05
SDP: 101
YPP: 01
ZLP: 16
Jimlar kuri'u masu inganci – 14,549
Lalatattun kuri'u – 234
Jimlar zaben da aka kada – 14,783
Akoko ta kudu maso yamma
Masu rijista — 107,651
Wadanda aka tantance – 36,383
A — 20
AA — 13
AAC — 26
ADC — 427
ADP — 91
APC — 28,367
APGA —37
APM — 10
APP — 16
BP — 7
LP — 920
NNPP — 28
NRM — 9
PDP — 5,376
PRP — 15
SDP — 161
YPP — 9
ZLP — 45
Jimlar kuri'u masu inganci — 35,577
Lalatattun kuri'u – 781
Jimlar zaben da aka kada– 36,358
A wani labari na daban, mun ji cewa wasu bata gari sun harbi mata biyu yayin gudanart da zaben shugaban kasa a jihar Bayelsa.
Asali: Legit.ng