Yemi Osinbajo ya isa gida domin kada kuri’a, alamu sun nuna wanda zai zaba a 2023
- Tun ranar Juma’a, mataimakin shugaban kasa ya isa garinsu da nufin ya kada kuri’a a zaben yau
- Daga zuwansa, Farfesa Yemi Osinbajo ya shiga yin taro da shugabannin jam’iyyar APC a gidansa
- Alamu sun nuna Osinbajo da magoya bayansa za su zabi Bola Tinubu da sauran ‘yan takaran APC
Ogun - Mai girma mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya isa garinsa domin ya kada zaben sabon shugaban kasa.
A matsayinsa na mai magana da yawun mataimakin shugaban Najeriya, Laolu Akande ya fitar da hotunan mai gidansa kauyensu a Twitter.
Laolu Akande ya tabbatar da Yemi Osinbajo ya isa mahaifarsa ta Ikenne da ke jihar Ogun a yammacin Juma’a, 24 ga watan Fubrairu 2023.
Daga zuwansa a ranar jaji-birin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya, Osinbajo ya yi zama na musamman da ‘yan jam’iyyar APC.
Wannan ya tabbatar da cewa Farfesa Osinbajo zai goyi bayan APC duk da rade-radin da ake yi na cewa bai goyon bayan takarar Bola Tinubu.
Zaben fitar da gwani a APC
Mataimakin shugaban kasar yana cikin wadanda Tinubu ya gwabza da su a zaben fitar da gwani, ya yi galaba a kan tsohon kwamishinansa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rashin ganin sunan Osinbajo a kwamitin yakin takarar shugaban kasa na APC ya jawo aka fara tunanin an samu baraka tsakaninsa da Tinubu.
Osinbajo ya shiga Egunrege
“A shirye-shiryen zaben kasa da za ayi gobe, mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya isa Ikenne da ranar nan.
Ya shiga taro da shugabannin APC da jagororin al’umma a gidansa. Zai yi zabe a akwati na 14 da ke Egunrege a Ikenne.
Masoya sun bi bayan PDP
Hakan na zuwa a lokacin da Tribune ta rahoto cewa kungiyar Osinbajo Support Group ta fito baro-baro, ta fadawa mutanenta su zabi Atiku Abubakar
Shugaba da sakataren wannan kungiya ta magoya bayan Osinbajo, Sunnie Chukumele da John Elemi sun fitar da jawabi cewa su na tare da PDP.
Jega ya yi magana a kan zaben yau
Za a ji labari cewa tsohon shugaban hukumar INEC a Najeriya ya jinjina shirin da aka yi, amma ya soki tsarin canza kudi da gwamnatin tarayya ta kawo.
A zaben 2023 akwai batun aika sakamakon zabe ta na’ura, dole bayanan INEC su shiga yanar gizo. Attajiru Jega ya ce hakan zai iya jawo ayi kutse.
Asali: Legit.ng