2023: Muhimman Abubuwa Da Ya Kamata Ku Sani Game da Dan Takarar Shugaban Kasa Na NNPP, Rabiu Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso, shine dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kwankwaso shine jagoran kungiyar Kwankwasiyya mai tarin magoya baya kuma ana gane mabiyansa ne da alamarsu ta jan hula.
A wannan zauren Legit.ng Hausa za ta kawo maku dan takaitaccen tarihi da muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da jagoran na kungiyar Kwankwasiyya masu jan hula.
1. Takaitaccen tarihin hihuwarsa
An haifi Sanata Rabiu Kwankwaso a ranar 21 ga watan Oktoban 1956, a yankin Kwankwaso da ke a karamar hukumar Madobi ta jahar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, rahoton Wikipidia.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Karatunsa
Kwankwaso ya yi karatunsa na Firamare a garin Kwankwaso, daga nan ya tafi makarantar kwana ta Gwarzo a jihar Kano.
Bayan nan ya tafi makarantar kere-kere da ke a garin Wudil da kuma kwalejin fasaha ta Kano kafin ya tafi makarantar kimiyya da fasaha ta Kaduna inda ya samu difloma da babbar difloma.
Har ila yau, Kwankwaso ya yi karatu a kwalejin Middlesex da ke birnin Landan, kasar Ingila a 1982 zuwa 1983.
Ya kuma ci gaba a jami’ar fasaha da ke Loughborough a kasar Ingila a 1983 zuwa 1985 inda ya samu digiri na biyu a fannin fasahar ruwa.
3. Kafin ya shiga siyasa
Kwankwaso ya yi aiki tare da hukumar albarkatun ruwa ta jihar Kano a 1975 inda ya shafe tsawon shekaru 17 yana aiki a bangarori daban-daban na hukumar har ya zama shugaban ma’aikatar.
4. Bayan ya shiga siyasa
A 1992 Kwankwaso ya shiga harkar siyasa karkashin inuwar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP). Ya kasance dan gaban goshi a bangaren SDP da Janar Shehu Yar’adua ke jagoranta.
An zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Madobi a 1992. Zabarsa da aka yi a matsayin mataimakin kakakin majalisa shine yasa ya yi suna a siyasar kasar.
Yayin taron gyara kundin tsari na 1995, an zabi Kwankwaso a matsayin daya daga cikin wakilan Kano.
5. Gwamnan Kano
Kwankwaso ya koma jam’iyyar PDP a 1998. An zabe shi a matsayin gwamnan jahar Kano a 1999 har zuwa 2003. Sai dai kuma ya sha kaye a hannun Ibrahim Shekarau lokacin da ya yi yunkurin zarcewa.
Bai yi kasa a gwiwa ba, Kwankwaso ya sake yin takarar gwamna a zaben 2011 inda ya yi nasarar lashe zabe a matsayin gwamnan Kano a karo na biyu.
6. Zaben shugaban kasa na 2014
Kwankwaso ya yi amfani da farin jininsa a Kano wajen yin takarar tikitin shugaban kasa na APC a zaben 2015 inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi nasara kuma ya yi masa mubaya’a.
Dani za a yi: Tsohon gwamnan jihar Arewa ya shiga jerin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa
7. Ministan tsaro
Gwantain tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta nada Kwankwaso a matsayin ministan tsaro daga 2003 zuwa 2007.
8. Sanatan Kano ta tsakiya
Tsohon gwamnan na Kano ya rike mukamin sanata mai wakiltan yankin Kano ta tsakiya daga watan Mayun 2015 zuwa Mayun 2019.
9. Zaben shugaban kasa na 2019
A watan Mayun 2018, Kwankwaso tare da gwamnonin APC 14 sun sauya sheka zuwa PDP. A watan Oktoban 2018, Kwankwaso ya yi takarar tikitin PDP a zaben fidda gwanin shugaban kasa.
Sai dai Alhaji Atiku Abubakar ne ya lashe zaben fidda gwanin inda Kwankwaso ya yi masa mubaya’a.
10. Farfado da jam’iyyar NNPP
A watan Fabrairun 2022, Kwankwaso ya kafa wata tafiya ta siyasa wanda ke adawa da manyan jam'iyyun siyasar kasar ta APC da PDP.
A haka ne ya farfado da jam’iyyar Nigeria Peoples Party (NNPP) mai kayan marmari inda ya zama shugaban jam’iyyar na kasa a ranar 30 ga watan Maris din 2022.
Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye
11. Tallafawa matasa
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya yi kaurin suna da samun karin farin jini sosai saboda shirinsa na tura daliban jiharsa ta Kano karatu a kasashen waje. ‘Ya’yan talakawa da dama sun amfana da wannan shiri nasa.
Asali: Legit.ng