Yadda Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso Za Su Raba Kuri’u Miliyan 87 Nan da Awa 24
- Yanzu sa’o’i kadan suka rage a shiga zaben sabon shugaban kasa wana zai gaji Muhammadu Buhari
- Alamu na nuna nasara ta na wajen Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi, ko kuwa Rabiu Musa Kwankwaso
- Canjin kudi, karfin jam’iyyu, Gwamnoni, addini da kuma kabilanci za su yi tasiri a kan zaben na Najeriya
Abuja - Jaridar nan ta Daily Trust ta fitar da dogon rahoto a kan yadda za a fafata a babban zaben gobe
Masana sun ce babu wani wanda ake da tabbacin zai lashe zaben, kuma kowane cikin manyan ‘yan takara hudu yana da cewa a kan kuri’u miliyan 87.
Farfesa Jibrin Ibrahim da wasu masana sun nuna tsarin canza kudi da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo zai yi tasiri a kan wanda zai lashe zaben.
Jami’an tsaro, labarai da yankin da ‘yan takara suka fito za su yi tasiri a cewar Idayat Hassan. Legit.ng Hausa ta na ganin addini zai yi matukar tasiri a gobe.
Rahoton ya nuna cewa zai yi wahala Atiku Abubakar ya yi galaba a kan Bola Tinubu a Borno da Yobe duk da ya fito daga Arewa maso gabashin kasar nan.
Gwamnonin APC za su taimaki Tinubu
Hassan ta ce ana kuma sa ran Gwamnoni 21 da APC take da su a fadin kasar za su yi sanadiyyar da Tinubu zai samu akalla 25% na kuri’un da ke jihohinsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ra’ayin da-dama daga cikin masu hasashe shi ne APC da PDP za su cika sharadin da ake bukata na kawo 25% na kuri’un masu kada zabe daga jihohi akalla 24.
Magoya bayan Atiku su na ganin tikitin Musulmi da Musulmi ba zai hana su nasara a Arewa ba, musamman yadda ba a maganar Peter Obi na LP a yankin.
Duk da haka irinsu Dr. Ahmad Adamu wanda hadimin ‘dan takaran PDP ne, ya yarda Sanata Rabiu Kwankwaso da NNPP za su yi masu lahani a wasu wurare.
Da aka zanta da Jide Ojo wanda mai sharhi ne a kan siyasa, ya ce kabilanci zai yi tasiri. Ana zargin kuri’un Ibo a Legas za su iya taimakawa Peter Obi sosai.
Baya ga Legas, mai sharhin ya ce za ayi yaki a kan kuri’u kusan miliyan shida da ke Jihar Kano. Alamu na nuna Kwankwaso ne ya fi kowa karfi a jihar Arewar.
Anya Kwankwaso zai kai labari?
Akwai masu ganin babu wanda ya cancanta irin Rabiu Musa Kwankwaso, sai dai da kamar wahala kuri’un NNPP su fito daga kowane bangaren Najeriya a gobe.
Farfesa Jideofor Adibe bai hango Kwankwaso a kan mulki, ya ce nasara ta na tsakanin Tinubu, Atiku ko dai Obi wanda dukkansu hamshakan Attajirai ne.
Jaridar ta ce zaben 2023 zai nuna karfin matasa da masu dumin kirji a dandalin sada zumunta. A kafar Twitter, kusan magoya bayan jam’iyyar LP sun fi yawa.
An yi wa Tinubu mubaya'a
A ranar Alhamis aka samu labari cewa an wasu Jam’iyyun adawa sun sanar da Bola Tinubu a matsayin ‘dan takaransu a zaben Shugabancin kasa da za ayi.
Ganin lokacin zaben shugaban Najeriya ya zo, jam’iyyun ZLP, APP da APM sun fadawa mabiyansu su zabi APC domin Tinubu ne wanda ya fi cancanta.
Asali: Legit.ng