Kalamansa Sun Jawo Masa, Za a Shiga Zabe, Kotu ta Daure ‘Dan Takara a Kurkuku

Kalamansa Sun Jawo Masa, Za a Shiga Zabe, Kotu ta Daure ‘Dan Takara a Kurkuku

  • ‘Yan Kwanaki suka rage a shiga filin zabe, amma ‘yan sanda sun cafke Dan Majalisa a Ribas
  • Da aka je Kotu, Alkali ya daure wanda ake tuhuma, Hon. Ephraim Nwuzi domin a iya yin bincike
  • Ana tuhumar ‘Dan takaran da cin amanar kasa, hada baki, da tada rikici, sai Maris za a saurari karar

Rivers - Wata kotun majalistare da ke zama a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas ta tsare ‘dan majalisar Etche/Omuma, Ephraim Nwuzi a kurkuku.

Rahoto daga Daily Trust ya tabbatar da Alkali ya umarci a rufe Hon. Ephraim Nwuzi a gidan gyaran hali saboda zargin cin amanar kasa da tada rikici.

Da aka zauna da nufin sauraron karar a kotu, Lauyan wanda ake tuhuma, Barista Emenike Ebete ya bukaci a ba shi belin ‘dan majalisar tarayyar.

Kara karanta wannan

Saura kiris zabe: Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka dasa bam a gidan TV da rediyo a jihar Ribas

Jami’an ‘yan sandan jihar Ribas da masu shigar da karar ba su amince da rokon Ebete ba, suka roki a tsare Hon. Nwuzi domin ayi bincike sosai.

Alkali ya ce a tsare wanda ake kara

Bayan sauraron kowane bangare, Mai shari’a O Amadi-Nna ya yi umarni a rufe ‘dan majalisar mai neman tazarce a gidan gyaran hali kafin a gama shari’ar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lauyan ‘dan siyasar ya fadawa manema labarai cewa zargin ba su cancanci a cafke wanda ake kara ba. Jaridar Vanguard ta fitar da wannan labari a dazu.

Masu zabe
Gidan yari da Masu zabe Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kamar yadda Ebete ya bayyana, Alkali ya ce za a cigaba da tsare wanda yake ba kariya har sai zuwa ranar 3 ga watan Maris da za a saurari tuhumar.

Yadda aka cafeko Hon. Nwuzi

This Day ta ce har gida ‘yan sanda suka shiga domin damko jigon na APC. Nwuzi yana zaune ne a garin Chokocho a karamar hukumar Etche da ke Ribas.

Kara karanta wannan

Zabe Ya Gabato, IGP ya yi Mamaya da Wasu Sauye-sauyen Kwamishinoni a Manyan Jihohi

Kafin nan an ji Kakakin rundunar ‘yan sanda na Ribas, Grace Iringe-Koko yana cewa AIG Abutu Yaro yana neman Nwuzi a bisa zargin wasu kalamai da ya yi.

Ana zargin an ji ‘dan siyasar mai wakiltar mazabar Etche da Omuma ya fada magoya bayansa su kai hari ga mutane har da jami'an INEC a lokacin yin zabe.

Rabiu Kwankwaso zai gama kamfe

Ku na da labari ‘Dan takaran NNPP, Rabiu Kwankwaso zai rufe kamfe a gida kamar yadda Bola Tinubu da Atiku Abubakar suka rufe a Legas da Adamawa.

Ana tunanin garin Kano zai cika da ‘Yan Kwankwasiyya da NNPP tun daga Kwanar Dangora. Sai dai APC ta tsaida ranar nan domin kammala yakin zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng