Atiku Ya Kara Caccakar Gwamna Wike, Ya Ce Gwamnan Ba Zai Iya Baiwa Tinubu Kuri'un Ribas Ba
- Alhaji Atiku Abubakar ya ayyana kwarin guiwarsa cewa gwamna Nyesom Wike ba zai iya gamsar da mutanen Ribas su zabi Tinubu ba
- Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP ya ce takarar Tinubu ba ta dace da muradin mazauna Ribas ba
- Atiku ya bayyana cewa Wike ya san Tinubu bai da masoya a jihar shiyasa ya gaza hitowa ya mara masa baya a fili
Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya ce gwamna Wike ba zai iya baiwa Bola Tinubu, ɗan takarar APC galaba a jihar Ribas a zabe mai zuwa ba.
Atiku ya yi wannan furucin ne ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin watsa labarai, Phrank Shaibu, ranar Talata 21 ga watan Fabrairu a Abuja.
Jita-jita ta yi ƙamari kan cewa gwamna Nyesom Wike ya umarci Sojojin siyasarsa su tabbata Tinubu ya lashe kuri'un jihar Ribas a zaben ranar Asabar.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa yayin zantawa da manema labarai, Mista Shaibu ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ko matacce ya san APC ba zata taba nasara a jihar Ribas ba, Wike ba zai kawowa Tinubu rumfarsa ta zaɓe ba. Ya san haka shiyasa ba zai iya bugun ƙirji ya umarci mazauna Ribas su zaɓi Bola Tinubu ba."
"Maimakon haka ya koma kewaye-kewaye yana hannunka mai sanda. Amaechi yana da zarrar fita daga PDP ya koma APC har ya yi wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari kamfe a 2015 kuma ya yaki ɗan yankinsa."
"Haka mutanen gaske suke yi idan suka gamsu da matsayarsu. Wike ya ce zai bayyana ɗan takarar shugaban kasan da yake so a watan Janairu, 2023, ga shi bayan watan har mako 3 sun wuce amma shiru."
Ya kuma yi zargin cewa dabarar Wike ɗaya, ranar zaɓe zai baiwa wasu baragurbi kuɗi su ta da zaune tsaye domin mutane su ji tsoron fitowa jefa kuri'a.
PDP ta fitittiki ɗan takararta na gwamna a Akwa Ibom
A wani labarin kuma Rigima ta ƙara tsananta a babbar jam'iyyar adawa, PDP Ta Kori Dan Takarar Gwamna a Jihar Akwa Ibom
Ɗan takarar gwamnan ya ja daga da wanda gwamna Udom Emmanuel ya tsayar domin ya gaje shi, lamarin da ake ta fafatawa a Kotu.
PDP reshen Akwa Ibom ta ce ta fatattaki ɗan takarar ne saboda ta gano yana amfani da Satifiket ɗin bogi.
Asali: Legit.ng