El-Rufai: Ba Adawa Muke Da Sauya Fasalin Naira Ba, Amma Buhari Ya Yi Kuskure

El-Rufai: Ba Adawa Muke Da Sauya Fasalin Naira Ba, Amma Buhari Ya Yi Kuskure

  • Gwamnan Kaduna, Nasir Elrufai ya ce ba saboda siyan kuri'a ne ya sa ba sa goyon bayan chanjin kudi ba
  • Gwamnan da ya ke zantawa da BBC Hausa ya ce akwai hanyoyin siyan kuri'a da yawan in shine dalilin da yasa basa goyon bayan dokar chanjn kudi
  • El-Rufai ya ce sun duba yadda mutane ke shan wahala ne kuma sun yadda anyi kuskure wajen zabar lokacin aiwatar da dokar

Mallam Nasiru El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kuskure wajen sauya fasalin kudi.

Da ya ke zantawa da BBC Hausa ranar Litinin, El-Rufai ya ce an kirkiri chanjin kudin ne don kayar da jam'iyyar APC zabe.

El-Rufai
El-Rufai: Ba Adawa Muke Da Sauya Fasalin Naira Ba, Amma Buhari Ya Yi Kuskure. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Ya ce gwamnoni ba sa goyon bayan dokar saboda wahalar da ta jefa talakawa a ciki ba wai saboda siyan kuri'a ba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya shirya yaki, ya fadi yadda zai hukunta bankin da bai karbar N500, N1000

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da yasa gwamnoni ba su goyon bayan sauya naira a yanzu, El-Rufai

El-Rufai ya ce:

''Mun duba yadda wannan dokar da wahalar da ta jefa mutane da yadda yan Najeriya su ka tsani jam'iyyar APC saboda suna kifa zargin akan jam'iyyar APC kuma wanda suka kirkiri dokar sun yi ne don kada jam'iyyar mu zabe.
''Bayan mun yi duba na tsanaki, mun amince da hukuncin kotun koli na cewa a ci gaba da amfani da tsoho da sabon kudi har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.
''Yau aka fara siyan kuri'a? Me yasa ba a chanja ba a baya? Me yasa sai yau? Abu na biyu, da iya naira ake siyan kuri'a? Za a iya siya da dalla, euro, sefa, ko ka bawa masu zaben abinci.
Akwai hanyoyi da dama da za a iya siyan kuri'a. Ba za ka hana amfani da kudi a siyasa ba, amma za ka iya rage wa."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shin Tinubu Yana Da Lafiyar Da Zai Iya Shugabancin Najeriya, El-Rufai Ya Bada Amsa

Gwamnan na Kaduna ya cigaba da cewa:

''Ba saboda siyan kuri'a ne ba ma goyon bayan wannan dokar ba. Wallahi saboda yadda muka ga mutane suna shan wahala ne, ba wai zabe ba.
''Wanda suka tilasta chanjin kudin nan ba yan APC ba ne. Ka ga Godwin Emifiele, PDP ce ta kawo shi. Mutanen da akayi shawara da su mun san su kuma idan lokaci ya yi, za mu bayyana su saboda ba yan jam'iyyar mu ba ne.
''Da yardar Allah ranar Asabar talakawa za su yi ramuwa akan wanda su ke son ganin bayan jam'iyyar APC da ta basu dama suka samu kudi fiye da kima da zai ishe su cefane saboda wasu a cikin su shekara takwas da ta gabata cefane wahala ya ke a gidajen su, amma yanzu, suna da kudi fiye da tunaninka."

Har wa yau, gwamnan na Kaduna ya cigaba da cewa:

Kara karanta wannan

El-Rufai: Yadda Yan Takarar Shugaban Ƙasa 2 Suka Samu Ɗaruruwan Sabbin Miliyoyin Takardun Naira

''Na rantse da Allah sai mun fito da su sai sun fada mana inda su ka samu kudin.
''Saboda shugaban kasa mutum ne mai yarda da mutane, mu kuma (gwamnoni), an bata mana suna. An gaya masa cewa gwamnoni barayi ne shiyasa bama goyon bayan chanjin kudi.
''Ko munje wajensa mun ce 'shugaba karya ake fada maka a wajen nan', kuma ya ce na gane kuma zan dauki mataki, muna tafiya, za a ce masa kada ka dauki wani mataki.
''Kowanne mutum tara ne bai kai goma ba. Anan wajen, mun yarda shugaban kasa ya yi kuskure.''

A wani rahoton kun ji cewa gwamnan na jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya jingine umurnin Shugaba Muhammadu Buhari game da sauyin fasalin kudi ya ce mutanen jiharsa su cigaba da kashe tsohon kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164