Zaben Shugaban Kasa: Tinubu Ya Zo Na Ɗaya, Obi Da Atiku Suna Biye Da Shi A Zaɓen Jin Ra'ayi
- Wani zaben gwaji ta shafin yanar gizo ya gwada yadda jam'iyyar APC da dan takarar ta Bola Tinubu, ke da yiwuwar lashe zabe
- Zaben gwajin da aka shafe sati 4 ana gudanarwa ya bayyana yadda kowanne dan takara ya samu kuri'a da kuma yankunan da ya lashe
- Hasashe ya bayyana cewa sabanin yadda wasu ke tunanin za a tafi zagaye na biyu, ana iya samun wanda zai ci zabe kai tsaye tun a zagayen farko
Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na da yiwuwar lashe zaben shugaban kasa mai zuwa a Najeriya, rahoton Leadership.
Hakan na kunshe cikin wani rahoton zaben gwaji na sati hudu, wanda wasu gamayyar masana tattara bayanai, da sanya idon FREDDAN suka gudanar da zaben jin ra'ayi na zaben 2023 ga yan takarar shugabancin kasa.
Zaben ya gudana tsahon sati hudu daga 7 ga Janairu zuwa 11 ga Fabrairu na 2023, ya nuna dan takarar APC, Bola Tinubu, a matsayin wanda zai lashe zaben. Tinubu, kamar yadda sakamako ya nuna, yana saman yan takarar jam'iyyar PDP, LP da kuma NNPP.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tawagar, yayin gudanar da zaben, sun yi amfani da kwararrun masana tattara bayanai, wanda suka yi amfani da yanar gizo don karbar bayanan masu zabe, Daily Trust ta rahoto.
Yadda aka gudanar da zaben jin ra'ayin
An gudanar da zaben ta hanyar shafin intanet mai cike da tsaro da zai iya hana maimaita kada kuri'a yayin da wasu ma'aikatan ke kula da shafin cikin manyan yarukan kasar nan - Igbo, Yoruba, Hausa don bawa masu zaben amsa a yaren da mutum ya zaba.
Zaben na FREDDAN ya tantance sama da tambayoyi 370,000 a tsahon sati 4 inda ya samu martani 287,033 a fadin jihohi 36 da kuma birnin tarayya.
Yiwuwar Nasarar Tinubu
Kididdiga ta nuna cewa dan takarar APC, Bola Tinubu, shi yake da kaso mafi yawa na yiwuwar lashe zaben shugaban kasa, inda ya samu kuri'a 106,764 a zaben gwajin, wanda ya kunshi kaso 37.2 na wanda suka kada kuri'a.
Zaben ya kuma nuna yadda Tinubu ya ke da rinjaye a mafi yawan sassan kasar nan, inda ya cinye jihohi 19 cikin 36.
Yadda ta kasance da Peter Obi, Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso a zaben jin ra'ayin
Dan takarar LP, Peter Obi, shi yazo na biyu da kuri'a 92,127. Hakan ya ba shi kaso 32.1 na wanda suka gudanar da zaben. Yayin da ya lashe jihohi 8 daga 36 a fadin kasar nan.
Dan takarar PDP, Atiku Abubakar, shi ne yayi na uku da kuri'a 88,109, inda yake da kaso 30.7 na masu kada kuri'ar. Ya kuma lashe jihohi 10 daga cikin 36 da ke fadin kasar nan.
Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP ne ya zo na hudu da tazara mai nisa, inda ya samu kuri'a 693, wanda ke nufin kaso 0.23 na wanda suka kada kuri'a.
Kamar yadda sakamakon zaben ya nuna, Tinubu na jam'iyyar APC zai iya lashe mafi rinjayen kuri'u a Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya, da Kudu maso Yamma.
Dan takarar PDP, Abubakar na da yiwuwar lashe babban birnin tarayya da kuma Kudu maso Kudu. Obi na jam'iyyar LP na da yiwuwar lashe yankin Kudu maso Gabas, yayin da za a kasafta kuri'un Arewa ta Gabas tsakanin APC da PDP.
Zaben gwajin yayi hasashen lashe zaben Bola Tinubu, a ranar 25 ga wata kuma yadda kuri'un ko wanne yanki suka nuna za a iya samun wanda zai lashe zaben a zagayen farko ba kamar yadda wani hasashen ke fadin za a tafi zagaye na biyu ba.
A wani rahoton, kun ji cewa Hajiya Maryam Salihu, jigo a jam'iyyar APC ta bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ba kudi ya ke nema, yana son shugabancin kasa ne don ci da kasar gaba.
Asali: Legit.ng