Mambobin LP A Arewa Maso Yamma Sun Watsar da Obi, Sun Koma Bayan Tinubu a 2023

Mambobin LP A Arewa Maso Yamma Sun Watsar da Obi, Sun Koma Bayan Tinubu a 2023

  • Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya kama hanyar mamaye kuri'un arewa maso gabas
  • Mambobin jam'iyyar LP da masu neman takara a shiyyar sun ayyana cikakken goyon bayansu ga tsohon gwamnan Legas
  • A ranar Asabar mai zuwa, 25 ga watan Fabrairu, 2023, hukumar INEC zata gudanar da zaben shugaban kasa

Kwanaki kalilan gabanin babban zaɓen 2023, mambobin Labour Party a arewa maso yamma, sun bayyana goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu.

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Mista Peter Obi, shi ne yake neman zama shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar LP, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Asiwaju Bola Tinubu.
Mambobin LP A Arewa Maso Yamma Sun Watsar da Obi, Sun Koma Bayan Tinubu a 2023 Hoto: Bola Tinubu
Asali: Facebook

Da yake jawabi a taron manema labarai a madadin ɗaukacin mambobin LP na shiyyar arewa maso yamma, Bashir Ishaq, ya ce a shirye suke su yi aiki domin Tinubu ya kai ga nasara.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Kutsa Wurin Taron Shugaban APC da Gwamnoni Sama da 10, Bayanai Sun Fito

Ishaq, wanda a yanzu ke jagorantar, 'Game Changers For Asiwaju/Shettima' ya ce a halin yanzun sun tattara kayansu sun koma jam'iyya mai mulki, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A jawabinsa ya ce:

"Gamayyar yan takarar gwamna, Sanatoci, majalisar wakilai da majalisar jiha, shugabanni da mambobin kwamitin kamfe, mambobin kamfen ɗan takarar gwamna Kano da arewa maso yamma na LP duk mun cimma matsaya."
"Baki ɗayanmu mun amince da goyon bayan takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Mun amince zamu maida shirinmu da tsarukan siyasar mu wajen haɗa kan al'umma har ya kai ga zama shugaban ƙasa na gaba."
"Daga yanzu za'a riƙa kiranmu 'Masu canja wasan domin Tinubu/Shettima' kuma taken mu shi ne, 'Lalubo kuri'u'. Daga karshe mun cimma matsayar komawa inuwar APC mai mulki."

Legit.ng Hausa ta tattaro maku cewa wannan ci gaban na zuwa ne kwana 5 gabanin zaɓen shugaban kasa wanda zai gudana ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Hadu Da Gagarumin Cikas a Arewa: Dan Takarar Gwamnan LP a Kano Ya Yi Maja a APC

An Nemi Wike An Rasa Yayin da Atiku Ya Gana Da Masu Ruwa da Tsakin PDP Na Ribas

A wani labarin kun ji cewa mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP ya zauna da masu ruwa da tsakin jihar Ribas a Abuja

Taron wanda ya gudana jiya Lahadi da daddare ya maida hankali ne kan yadda PDP zata samu galaba a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Har yanzun ba'a ga maciji tsakanin shugabancin PDP da Wike kuma gwamnan bai halarci ganawa da Atiku ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262