Zaben 2023: Bamu Kulla Kwance da Jam'iyyar PDP Ba, Al-Mustapha

Zaben 2023: Bamu Kulla Kwance da Jam'iyyar PDP Ba, Al-Mustapha

  • Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya karyata labarin da ke yawo game da jam'iyyar AA
  • Al-Mustapha, mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar AA ya ce jam'iyyarsa ba ta kulla kawance da Atiku ba
  • Tsohon dogarin tsohon shugaban kasa ya ce ba gudu ba ja da baya zasu shiga zaɓen 2023 nan da yan kwanaki

Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar Action Alliance (AA) a zaɓen 2023, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya musanta rahoton dake cewa jam'iyyarsa ta hakura ta marawa Atiku Abubakar na PDP baya.

A wurin ralin karkare kamfen shugaban kasa na PDP da ya gudana a Adamawa ranar Asabar, shugaban jam'iyyar APM na kasa, Yusuf Dantele, ya ce jam'iyarsa da wasu 4 sun janyewa Atiku.

Hamza Al-Mustapha.
Zaben 2023: Bamu Kulla Kwance da Jam'iyyar PDP Ba, Al-Mustapha Hoto: dailytrust

Dantele, wanda ya ce ya faɗi haka ne a madadin sauran jam'iyyun, ya lissafa su kamar haka, Action Peoples Party (APP), National Rescue Movement (NRM), the African Democratic Congress (ADC) da jam'iyar AA.

A cewarsa waɗan nan jam'iyyun sun janye daga shiga takarar shugaban kasa kana sun koma bayan wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar, rahoton Daily Trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bugu da ƙari, ya sanar da cewa sun zauna sun cimma wannan matsayar ta goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP saboda, "Shi ne wanda ya cancanta da mulkin Najeriya."

Ba gaskiya bane - Hamza Al-mustapha

A wata hira yau Lahadi, Al-Mustapha ya yi kira ga yan Najeriya su yi fatali da masu kirkirar labaran ƙarya waɗanda basu da aiki sai haddasa ruɗani da yaɗa Farfaganda.

Da yake jawabi ga manema labarai ta bakin mai magana da yawunsa, Chidi Edom, Al-Mustapha, ya roki masoyan AA, 'yan takara da miliyoyin magoya baya a ciki da wajen kasar nan su yi fatali da labarin.

Nairaland ta rahoto Almustapha na cewa:

"Munsan masu ɗaukar nauyi kuma basu da alaƙa kwata-kwata da jam'iyyarmu, jininsu ya hau ne ganin manufofinmu da goyon bayan da muke samu a lungu da sako na kasar nan."
"Muna fatan basu mamaki a akwatunan zaɓe nan gaba kaɗan domin muna nan kan dugadugin mu ba abinda zai ɗauke mana hankali ko kawar da tunaninmu daga yunkurin samar da shugabanci nagari a ƙasar mu."

Ka taimaka mana lokacin matsalar Boko Haram - Zulum ga Tinubu

A wani labarin kuma Gwamna Zulum ya bayyana irin taimakon da Tinubu ya yi wa Borno lokacin da Boko Haram ke kan ganiyarta

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya yabawa ɗan takarar shugaba ƙasa na APC, Bola Tinubu, kan ayyukan alherin da ya yi ma Borno.

Zulum ya ce tsohon gwamnan Legas ya wuce a kirasa da abokin Borno sai dai Amini wanda ya tsaya kai da fata lokacin da Boko Haram ke cin karenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel