Bincike Ya Tono Bayahuden da Ya Shirya Magudi Domin Jonathan Ya Yi Nasara a 2015
- Wani daga cikin magoya bayan Goodluck Jonathan ya dauki hayar SCL domin a taimakawa PDP a 2015
- A dalilin haka aka dauko kamfanin Cambridge Analytical da nufin hana APC karbe mulkin kasar nan
- Bincike ya nuna wani Bayahude a Tel Aviv ya yi aikin kashewa Muhammadu Buhari kasuwa a APC
Abuja - Bincike da The Guardian UK ta gudanar, ya gano mutumin kasar Israila da ya yi wa Cambridge Analytical aiki domin a murde zabe a Najeriya.
Ana zargin kamfanin Birtaniyar nan na Cambridge Analytical ya yi yunkuri wajen birkita zaben shugaban kasa da APC ta lashe a watan Maris na 2015.
Binciken da aka yi ya nuna sunan wannan Bayahude da ya nemi ya yi wa zaben kutse shi ne Jorge. Babu wani karin bayani da aka samu a kan shi.
The Cable ta ce Jorge da mutanensa sun yi aiki tare da Cambridge Analytical a boye domin ganin Goodluck Jonathan ya zarce kan karagar mulki a Najeriya.
An dauko hayar SCL
A baya an ji yadda wani Attajiri da yake goyon bayan Shugaba Goodluck Jonathan ya dauki hayar kamfanin SCL aiki domin bata sunan Muhammadu Buhari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
SCL ya yi amfani da kamfaninsa na Cambridge Analytical wajen samun bayanan sirri a kan Buhari a lokacin yana takara, aka nemi a kashe masa kasuwa.
Wannan kamfani na Birtaniya ya yi bakin kokarinsa wajen fito da wasu bayanai da suka shafi harkar lafiya da kudi domin ganin ‘dan takaran bai karbu ba.
Tal Hanan ya shigo cikin lamarin
Guardian ta saki rahoton binciken da ta gudanar wanda ya nuna mata Jorge yaran Tal Hanan ne wanda ya kware a wajen yin kutse da yada labaran bogi.
Wannan Bayahude yana aiki ne daga wata tasha da ke wajen birnin Israila na Tel Aviv. Amma babu tabbacin Shugaba Jonathan ya san da zaman Jorge.
Aikin da Jorge ya rika yi wa Shugaban kasar kuma ‘dan takaran PDP a lokacin shi ne aika sakonni a boye domin taimakawa jam’iyya mai mulki ta ci zabe.
Rahoto ya nuna daga cikin aikin da aka yi lokacin har da yin kutse cikin wayoyin wasu jagororin jam’iyyar APC, Lai Mohammed ya fada cikin tarkon nan.
An yi ta yin taro iri-iri a Landan, Davos da Abuja domin ganin an karkato da hankalin masu zaben Najeriya domin su ki kada kuri’a ga Muhammadu Buhari.
Satar Diepreye Solomon Peter Alamieyeseigha
An samu rahoto Amurka ta dawo da Biliyoyin kudin da Marigayi Diepreye Alamieyeseigha ya sata da baitul-malin Bayelsa, ya ajiye a kasar waje.
Mutanen Bayelsa za su amfana da dukiyar ‘Dan siyasar da Goodluck Jonathan ya yi wa afuwa bayan satar $900, 000, za a gyara asibotocin da ke mahaifarsa.
CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya
Asali: Legit.ng