El-Rufai Ya Fasa Kwai Ya Bayyana Ainihin Niyyar Masu Sauya Fasalin Kudi

El-Rufai Ya Fasa Kwai Ya Bayyana Ainihin Niyyar Masu Sauya Fasalin Kudi

  • Gwamnan jihar Kaduna yace sauya fasalin takardun kuɗin naira wata kitumurmura ce da aka shirya domin ganin Tinubu ya faɗi zaɓe
  • Gwamnan yace waɗanda suka kitsa wannan kitumurmurar na jin zafin kayem da suka sha ne a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC
  • El-Rufai yace burin su shine su bore ya ɓarke a ƙasa ta yadda sojoji za su yi juyin mulki

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ƙarancin takardun kuɗi da rashin man fetur wani shiri ne da aka kitsa domin hana zaɓe a ƙasar nan ta yadda za a samar da gwamnatin wucin gadi.

A wani jawabi da El-Rufai yayi ga ƴan jihar sa a ranar Alhamis, yace wannan matsalar ƙarancin kuɗin da ake fama da ita, na daga cikin zagon ƙasan da ake yi domin ganin cewa Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyr APC, ya faɗi zaɓe. Rahoton The Cable

Kara karanta wannan

Aisha Ta Goyi Bayan Shawaran Da Tinubu Ya Bada Kan Sabbin Kuɗi, Tayi adawa da na Shugaba Buhari

Rufa'i
El-Rufai Ya Fasa Kwai Ya Bayyana Ainihin Niyyar Masu Sauya Fasalin Kudi
Asali: Twitter

“Yana da kyau mutanen jihar Kaduna da Najeriya gabaɗaya, su sani cewa saɓanin maganganu da ake gaya musu cewa da zuciya ɗaya aka fito da wannan tsarin, wannan tsarin waɗanda suka sha kaye ne a zaɓukan fidda gwani na gwamna da shugaban ƙasa, suka kitsa shi suka ba shugaban ƙasa." A cewar El-Rufai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Asiwaju Bola Tinubu na zama ɗan takarar da yayi nasara a watan Yuni 2022, sannan ya ƙi ɗaukar ɗaya daga cikin su a matsayin mataimaki, sai kawai aka kitsa wannan sauya fasalin takardun kuɗin domin ganin Tinubu bai yi nasara ba."
"Sun kuma so su cimma ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan guda uku: Samar da ƙarancin kuɗi a ƙasa gabaɗaya ta yadda ƴan Najeriya za su ƙi zaɓar ƴan takarar jam'iyyar APC, ta yadda jam'iyyar zata sha mugun kaye."

Kara karanta wannan

Duk Wanda Ya Cinyemun Kuɗi Kuma Ya Ƙi Zaɓena Zai Sheƙa Barzahu, Ɗan Takarar PDP a 2023

“Tabbatar da cewa ƙarancin kuɗin yayi ƙamari tare da matsalar rashin man fetur da ake fama da ita tun watam Satumban 2022, ta yadda ba za a gudanar da zaɓen 2023 ba, domin ƙafa gwamnatin wucin gadi wacce wani tsohon Janar zai jagoranta.
“Ganin an cigaba da samun ƙarancin man fetur, abinci, da wasu abubuwan buƙata na yau da kullum, wanda hakan zai sanya a samu zanga-zanga, rikici da karya doka da oda, ta yadda sojoji za su yi juyin mulki."

Jerin Sunayen Ƴan Takara 7 Da Suka Mutu Ana Dab Da a Fara Zaɓen 2023

A wani labarin na daban kuma, mun tattaro muku jerin sunayen ƴan takarar da suka rasu ana dab da a fara zaɓen 2023.

Ƴan takarar sun fito ne dai daga jam'iyyu daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel