Jam'iyyar APC Ta Rasa Wasu Manyan Jiga-Jigan Ta a Jihar Bauchi

Jam'iyyar APC Ta Rasa Wasu Manyan Jiga-Jigan Ta a Jihar Bauchi

  • Jam'iyyar APC a jihar Bauchi ta samu gagarumin koma baya, bayan da wasu jiga-jiga daga cikin ta suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP
  • Sun bayyana cewa shiri mai kyau da jam'iyyar PDP ke da shi ga mutanen jihar, shine ya janyo ra'ayoyin su zuwa cikinta.
  • Sun sha alwashin bayar da dukkanin gudunmawar da ta dace wajen ganin jam'iyyar PDP tayi nasara a zaɓen dake tafe

A yayin da zaɓen gwamnoni ke ƙara ƙaratowa, wasu ƴan kwamitin gudanarwa mutum 6 na yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Bauchi, a ƙarƙashin jam'iyyar APC, sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP.

Sauya sheƙar ya samar da wani babban koma baya ga takarar da Sadique Abubakar, ɗan takarar gwamnan APC na jihar. Rahoton jaridar Leadership.

PDP da APC
Jam'iyyar APC Ta Rasa Wasu Manyan Jiga-Jigan Ta a Jihar Bauchi
Asali: Twitter

Shugaban su, kwamared Nasiru Khalid, shine ya bayyana hukuncin su na ficewa daga jam'iyyar a ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Bayan Shan Kashi a Zaɓe, Sanatan NNPP Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa PDP a Jihar Bauchi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa shirin cigaba da jam'iyyar PDP mai mulki a jihar take da shi, shine ya janyo ra'ayin sa zuwa jam'iyyar, inda ya ƙara da cewa zasu bayar duk irin gudunmawar da ta dace domin ganin jam'iyyar tayi nasara a jihar.

Khalid yace sun cimma shawarar koma jam'iyyar PDP ne bayan sun tattauna da mabiyan su.

Yace tawagar su zata cigaba da nemo wa ƴan takarar jam'iyyar PDP ƙuri'u, duba da shirin da jam'iyyar take da shi, wanda a cewar sa zai amfani mutanen jihar.

Karya Ne, Babu Wanda Ya Yiwa Mai Mala Buni Rajamu: Ahmad Lawan

A wani labarin daban, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karyata rahotannin cewa an tayar da tarzoma a wajen taron kamfen jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Gashua, karamar hukumar Bade ta jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Goyon Bayan Tinubu: Ɗan Takarar Gwamnan Labour Party Na Ruwa, Jam'iyyar Na Shirin Juya Masa Baya

Mai magana da yawun Ahmad Lawan, Ola Awoniyi ya fitar da jawabi ranar Lahadi a Abuja, rahoton TheNation.

Ya bayyana cewa karerayi kawai yan jarida suka yada cewa an yiwa gwamna Mai Mala Buni jifar shaidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel