PDP, APC, LP: Shehu Sani Ya Faɗi Jam'iyyar Da Ya Kamata Gwamnoni Da Ke Fushi Da Jam'iyyarsu Su Shiga
- Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya aika sako ga gwamnonin Najeriya wadanda ba su ji dadin abin da shugaban jam'iyyarsu ke yi
- Dan siyasar ya bukaci gwamnonin da ke fushi da jam'iyyarsu su shiga jam'iyyar African Action Congress, AAC, ta Omoyele Sowore
- Tunda farko, Shehu Sani ya yi kira ga matasa a kasar su dena duk wani nau'in zanga-zanga yana mai cewa tarko ne da aka kafa don samun dalilin kin zaben 2023 a yayin da karancin mai da naira ke damun al'umma
Dan siyasa kuma lauya mai rajin kare hakkin bil adama, Shehu Sani ya yi kira ga gwamnonin Najeriya wadanda ke da matsala da shugabannin jam'iyyar su, su koma jam'iyyar African Action Congress, AAC, ta Omoyele Sowore.
A cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter da Legit.ng ta gani a ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu, tsohon sanatan na Kaduna ya shawarci gwamnonin da ke fushi da jam'iyyarsu a yayin da zabe ke tafe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shehu Sani ya shawarci gwamnonin Najeriya wadanda ke fushi da tsarin jagorancin shugabannin jam'iyyun su
Rubutun da ya yi a Twitter ta ce:
"Gwamnonin da ke fushi da jam'iyyar su su tafi su hada kai da jam'iyyar gwagwarmaya ta dan uwa Sowore inda babu rikici. Su yi shirin zuwa kotu a kullum, zuwa gudu duk sati da kuma yin zanga-zanga duk wata."
Yan Najeriya sun yi martani:
Yan Najeriya sun yi amfani da shafinsu na Twitter sun yi martani ga kalaman tsohon sanatan.
@Patricksunday3 ya rubuta:
"Sowore yana rawa domin tarbar tsaffin gwamnonin G5."
@dennisuchenna_ ya rubuta:
"Tun da akwai kwarankwatsa a APC da PDP ba."
@Didynne ya rubuta:
"Na ji kamshin rikici."
@anienime ya rubuta:
"Na rantse! Dariya ya kama ni. Wannan mutumin! Daga ina ka ke samun irin wannan rahar? Walllahi kana da ban dariya!."
@JohnIwuajoku ya rubuta:
"Jam'iyyar da dan takarar shugaban kasa shine shugaban jam'iyya kuma shine shugaban gangamin neman tallafi."
Hukuncin karshe da babban kotun tarayya ta yanke kan yin babban zaben 2023
A wani rahoton kun ji cewa kotun tarayya ta birnin tarayya Abuja ta yi fatali da karar da aka shigar a gabanta na neman hana yin babban zaben 2023.
An shigar da wannan karar neman hana yin zaben ne kan dalilin hana yan Najeriya mazauna kasashen waje yin zaben daga can kasashen da suke zaune.
Asali: Legit.ng