Atiku Abubakar Zai Kammala Yaƙin Neman Zaɓen Sa a Ranar Asabar
- Jam'iyyyar PDP ta shirya tsaf domin kammala yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a ranar Asabar
- Jam'iyyar zata gudanar da wannan gagarumin taron gangamin yaƙin neman zaɓen ne a jihar ɗan takarar ta na shugaban ƙasa
- Ya zuwa yanzu dai jam'iyyar ta zaga jihohi 33 na Najeriya domin tallata ɗan takarar ta
Babbar jam'iyyar hamayya ta Najeriya, Peoples Democratic Party (PDP), ta bayyana cewa ɗan takarar ta mai neman kujerar shugaban ƙasa zai kammala yaƙin neman zaɓen sa a ranar Asabar.
PDP ta sanar da cewa Atiku Abubakar zai kammala yaƙin neman zaɓen sa ne a jihar Adamawa, a ranar Asabar dake tafe, wanda zai gudana a dandalin Mahmud Ribadu, a Yola, babban birnin jihar. Rahoton The Cable

Asali: Depositphotos
Sanawar hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da wani darekta a kwamitin yaƙin neman shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Umar Bature, ya fitar.
A cikin sanarwar an nemi mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam'iyyar, gwamnoni, ƴan majalisu da shugabannin gudanarwa na jam'iyyar da su halarci wajen yaƙin neman zaɓen.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ku daure ku taho da gangamin magoya bayan ku, su kasance a wurin domin haɗa hannu da hannu da ɗan takarar mu na shugaban ƙasa, H.E. Atiku Abubakar, GCON, (Waziri Adamawa) domin ceto Najeriya." A cewar sanarwar.
Ya zuwa yanzu dai, jam'iyyar PDP tayi gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihohi 33 da birnin tarayya Abuja, a yayin da ta shirya gudanar da yaƙin neman zaɓen ta na kusa da na ƙarshe a ranar Alhamis, a jihar Taraba.
Sai dai, jam'iyyar bata samu damar gudanar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ba a jihar gwamna Wike wato Rivers.
Gwamna Wike Ya Kore Yuwuwar Sulhu Tsakanin G5 da Atiku Gabanin Zaɓen 2023
A wani labarin na daban kuma, gwamna Wike mai takun saƙa da Atiku Abubakar ya kore yiwuwar yin sulhu a tsakanin su, ana dab da a fara zaɓe.
Gwamnan ya kuma kulle ƙofa ga duk wata irin tattaunawa da ƴan tsagin Atiku Abubakar.
Asali: Legit.ng