Duk da ‘Danuwansa Yana Takarar Gwamna, Garo Ya Ce Ba Zai Zabi Jam’iyyar APC ba

Duk da ‘Danuwansa Yana Takarar Gwamna, Garo Ya Ce Ba Zai Zabi Jam’iyyar APC ba

  • Bello Sule Garo zai zabi NNPP daga sama har kasa a zaben da za a shirya a Fubrairu da Maris
  • Ko da babu wanda zai dangwalawa jam’iyyar NNPP kuri’arsa, Bello Sule Garo ya ce ya ji – ya gani
  • Matashin ba zai zabi APC ba, duk da yayansu watau Murtala Sule Garo yana takara a jihar Kano

Kano - Bello Sule Garo ya bayyana cewa a zabe mai zuwa da a za a shirya, kuri’arsa ta na wajen jam’iyyar hamayya ta NNPP.

Da yake magana a shafinsa na Twitter a Ranar Asabar Bello Sule Garo ya tabbatar da cewa yana tare da jam’iyya mai kayan dadi.

Bello Garo yake cewa ko da babu wanda zai zabi Rabiu Musa Kwankwaso, shi yana goyon bayan ‘dan takaran shugaban kasar.

“Katin PVC na na Kwankwaso ne, ko da kuwa ni kadai ne zan kada masa kuri’a, idan Allah ya so.”

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso ya Ziyarci Jihar Arewa Sau 2 a Kwana 15 Domin Samun Kuri’u a NNPP

- Bello Sule Garo

An raba jiha da 'danuwa?

Abin da zai ba wasu mamaki shi ne ‘danuwansa, Murtala Sule Garo yana neman kujerar mataimakin Gwamnan Kano a APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta fahimci Alhaji Sule Garo, suruki ne ga Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi gwamna sau biyu a jihar Kano.

Jam’iyyar APC ba
Rabiu Kwankwaso Hoto: @baba, Kwankwason Twitter
Asali: Twitter

Yayin da Murtala Garo yake neman mataimakin Gwamna a karkashin APC, Nasiru Garo da Bello Garo su na tare da Kwanwaso.

Ganin haka ta sa muka tambayi Bello Garo ko zai zabi jam’iyyar NNPP sak, ba zai yi wa ‘danuwansa kara a takarar Gwamna ba.

Wannan Bawan Allah ya tabbatar mana lallai jam’iyya mai kayan dadi za ta samu kuri’unsa a sauran zabukan majalisa da na jiha.

Wannan na mu ne - Kwankwaso Twitter

Abdullahi Ibrahim wanda ya yi suna wajen tallata Rabiu Kwankwaso a dandalin Twitter, ya tofa albarkacin bakinsa a kan batun.

Kara karanta wannan

2023: Kano, Kaduna da wasu jihohi 5 na Arewa duk na Tinubu ne, mataimakin shugaban APC

Malam Abdullahi ya ce ka da sunan ya rudi mutum, Bello Garo yana cikin magoya bayan NNPP da madugun darikar Kwankwasiyya.

Malam Bello Garo yana cikin ‘yan sashen shafukan sada zumunta na kwamitin yakin takarar Abba Kabiru Yusuf a zaben jihar Kano.

Shinkafa da waken Gumsu Abacha

A baya an ji labari 'Diyar tsohon Shuaban Najeriya, Gumsu Abacha ta ce a 2023, Kano sai ‘Dan Soja, a Katsina kuma sai Lado Danmarke.

Gumsu Abacha ta na goyon Muhammad Abacha da Lado Danmarke a PDP domin dayansu 'danuwanta ne, dayan kuma surukinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng