Matsala Ta Kunno, Jam'iyyar PDP Ta Soke Gangamin Kamfen Atiku a Ribas

Matsala Ta Kunno, Jam'iyyar PDP Ta Soke Gangamin Kamfen Atiku a Ribas

  • Kwamitin shugagan kasa a PDP ya soke ralin Atiku a jihar Ribas saboda dalilan da suka danganci tsaro
  • PCC-PDP ya ce Atiku ya amince da soke ralin ne saboda baya son zubar da jinin magoya bayansa a wurin
  • Gwamna Wike da Atiku Abubakar sun raba jaha ne tun bayan kammala zaben fidda gwanin PDP

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP a jihar Ribas ya soke gangamin kamfen Alhaji Atiku Abubakar wanda aka tsara gudanarwa ranar 14 ga watan Fabrairu, 2023.

Sanata Lee Meaba, wanda ya yi jawabi a madadin kwamitin a Patakwal, ya ce ba za'a gudanar da ralin kamfen ba a Ribas kwata-kwata saboda dalilan da suka shafi tsaro.

Gwamna Wike da Atiku.
Matsala Ta Kunno, Jam'iyyar PDP Ta Soke Gangamin Kamfen Atiku a Ribas Hoto: Nyesom Wike
Asali: UGC

Mista Meaba ya bayyana cewa Atiku, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, ya sanar da tawagar kamfe cewa ba ya son a zubar da jini a Ribas, shiyasa ya soke ralin.

Kara karanta wannan

Da Gaske Matasa Sun Yi Wa Gwamna Buni Ruwan Duwatsu? Gwamnatin Yobe Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

Punch ta rahoto Sanata Meaba na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Nasarar da muke fata da tsammanin Atiku Abubakar zai samu a zaɓe ba ta kai darajar jinin mutum ɗaya namiji ko mace a jihar Ribas ba."

Makon da ya gabata aka kaiwa DG Kamfe hari

Rahoton Daily Trust yace idan zaku iya tunawa a makon da ya gabata aka farmaki shugaban kwamitim kamfen Atiku na jihar Ribas, Dakta Abiye Sekibo, a Patakwal.

Sekibo ya zargi 'yan sandan da ke aiki a gidan gwamnatin Ribas da hannu a harin da aka kai masa amma gwamna Nyesom Wike, ya fito ya musanta.

Tun da fari gwamna Wike ya soke amincewar ya yi wa kwamitin kamfen Atiku su gudanar da Rali a Filin wasan Adokiye Amiesimaka amma daga baya ya canza tunani.

Ya ce gwamnatinsa ta sake amincewa su yi amfani da katafaren filin wasan ne bayan wasu manyan mutane sun roki alfarma.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Atiku Abubakar Ya Roki Jami’an Tsaro Su Cafke Tsohon Jigon PDP

Wike da Atiku sun samu saɓani ne tun bayan da gwamnan na jihar Ribas ya sha ƙasa a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa a zaben fidda gwanin PDP.

Tawagar Gwamnonin G-5 Ba Su Goyon Bayan Bola Tinubu, Jang

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan jihar Filaato ya ce tawagar gwamnonin G-5 ba su tare da takarar Bola Tinubu na APC

Jomah Jang, ya bayyana haka ne yayin da yake martani ga gwamnan Filato kuma DG na kwamitim kamfen Tinubu/Shettima, Simon Lalong.

Mista Jang ya ce tuni 'yan Najeriya suka daina kama maganganun Lalong kuma ga dukkan alamu mafarki ya yi G5 sun goyi bayan Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262