Babban Banki CBN Ya Musanta Barazanar Rufe Wasu Bankunan Ajiya

Babban Banki CBN Ya Musanta Barazanar Rufe Wasu Bankunan Ajiya

  • CBN ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa yana shirin garkame wasu bankuna saboda karancin takardun naira
  • A wata sanarwa, babban bankin ya ce babu wani abu makamancin haka kuma ya bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da batun
  • Bayan haka ya karyata rahoton dake yawo cewa gwamnan CBN yace babu kayan aikin buga sabbin naira

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya musanta raɗe-raɗin barazanar rufe wasu Bankunan kasuwanci saboda ƙarancin takardun sabbin naira.

CBN ya karyata jita-jitar ne a wata sanarwa mai ɗauki da sa hannun Osita Nwanisobi, daraktan sashin yaɗa labarai, wacce bankin ya wallafa a shafin Tuwita.

Babban banki CBN.
Babban Banki CBN Ya Musanta Barazanar Rufe Wasu Bankunan Ajiya Hoto: CBN

Sabuwar sanarwan ta bayyana cewa jita-jitar ba gaskiya bane kuma ta saɓa wa tsarin aikin bankuna a Najeriya.

Wani sashin sanarwan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Canza Fasalin Kuɗi Na Iya Kawo wa Sojoji Tasgaro a Ayyukan su - NSA Monguno

"Akwai wani sakon murya dake yawo a soshiyal midiya cewa CBN na shirin kulle wasu bankuna musamman a wata shiyya guda ta ƙasar nan."
"Muna sanar da cewa babu wani shiri makamancin wannan kuma zargin ba shi da tushe belle makama sannan ya saɓa wa tsarin ayyukan banki a Najeriya."
"Bisa haka muna kira ga ɗaukacin al'umma da su yi fatali da abinda sakon ya ƙunsa domin ba shi da alaƙa da CBN kuma an kirkiro shi ne domin tunzura mutane."

Shin dagaske CBN ba shi da kayan aikin buga sabon naira?

Tun a farko a cikin Sanarwan, CBN ya yi fatali da rahoton dake yawo cewa gwamnan Bankin, Godwin Emefiele, ya ce babu isassun takardun da za'a buga sabbin kuɗi.

Rahoton ya yi ikirarin cewa gwamnan CBN ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi a taron majalisar magabata ta ƙasa ranar Jumu'a a Aso Villa.

Amma CBN ya karyata zancen baki ɗaya da cewa:

Kara karanta wannan

"Laifin 'Yan Najeriya Ne" CBN Ya Fasa Kwai, Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa Kan Karancin Sabbin Naira

"Muna bayyana cewa babu inda gwamnan CBN ya faɗi haka yayin jawabinsa a taron majalisar magabata ta ƙasa ranar Jumu'a 10 ga watan Fabrairu, 2023."
"Abinda ya faru, Emefiele ya shaidawa mahalarta taron cewa sashin NSPMC na kokarin buga sabbin takardun domin gansar da bukatun 'yan Najeriya."

A wani labarin kuma Antoni Janar ya bayyana cewa ya kamata a rika duba amfanin sauya fasalin naira ba illa kaɗai ba

Da yake hira a gidan Radio Najeriya Kaduna, Ministan Shari'a kuma Antonu Janar, Abubakar Malami, ya ce sabon tsarin ya rage yawaitar garkuwa da mutane.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin tarayya zata yi biyayya ga umarnin Kotun koli na dakatar da haramta tsohon kuɗi har sai ta yanke hukuncin ƙarshe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel