Karancin Kudi: Batutuwa Uku Da Ya Dace Ku Sani Game da Matsayin Tsoho Da Sabon Naira

Karancin Kudi: Batutuwa Uku Da Ya Dace Ku Sani Game da Matsayin Tsoho Da Sabon Naira

'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan karancin takardun naira a hannu kuma suna tunanin yaushe takardun kudin da CBN ya sauya zasu wadata don harkokin kasuwanci su kankama.

Tun a watan Nuwamba, lokacin da babban bankin Najeriya (CBN) ya fito da sabbin takardun naira ake ta kai kawo kan yadda za'a aiwatar da sabon tsarin da kuma amfanin shi ga talaka.

Abun takaicin wa'adin da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya gindaya bisa amincewar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jefa 'yan Najeriya cikin ƙuncin rayuwa.

Gwamnan CBN da Buhari.
Karancin Kudi: Batutuwa Uku Da Ya Dace Ku Sani Gane da Matsayin Tsoho Da Sabon Naira Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Da fari Emefiele ya gindaya wa'adin 31 ga watan Janairu, 2023, amma ruɗani ya yawaita kuma masu ruwa da tsaki suka rika kiraye-kiraye a kunnen FG cewa ta bar tsoffin kuɗin su cigaba da amfani.

Sun shawarci gwamnatin tarayya kada ta haramta amfani da tsohon takardun kuɗin ta bi a hankali a hankali wajen janyesu daga hannun jama'a.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: CBN Ya Fitar Da Sabuwar Sanarwa Kan Karancin Naira, Ya Musanta Barazanar Rufe Bankuna

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ta tattaro maku muhimman batutuwan gaskiya guda uku da ya dace ku sani.

1. Shin CBN zai bar tsofaffi da sabbin takardun naira su cigaba da amfani a tare?

Akwai alamu masu karfi da suka nuna CBN ba zai bari tsofaffi da sababbin takardun naira su ci gaba da zama ana amfani da su ba kamar yadda Burtaniya ta Saudiyya suka yi.

Zamu iya cewa hakan ya fito a zahiri ne sakamakon sanarwan CBN cewa ya shirya buga karin takardun naira domin su wadata a hannun yan Najeriya.

A wasu hirarraki da ya yi, gwamna Nasiru El-Rufa'i na Kaduna ya yi zargin cewa gwamnan CBN na da wata ɓoyayyar manufa ganin yadda ya buga takardun biliyan N300bn bayan ya karbi kusan Tiriliyan biyu daga hannun mutane.

2. Har yanzu ya halasta a karbi tsoffin kuɗi?

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Ya Fusata, Ya Umarci a Kama Duk Wanda Ya Ƙi Karban Tsoffin Kuɗi

Kotun ɗaukaka kara ta dakatar da gwamnatin tarayya daga shirinta na janye tsohon kuɗi daga hannun mutane kuma shugaban kasa Buhari ya lashi takobin bin umarnin Kotu.

Sai dai a halin yanzu, 'yan kasuwa a wasu sassan ƙasar nan sun daina karban tsofaffin N200, N500 da N1000.

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya umarci a kama duk wanda baya karban tsohon naira a jiharsa.

3. Sai yaushe CBN zai wadata mutane da sabon naira?

Babban bankin ƙasa bai bayyana takaimaiman lokacin wadatar kuɗin ba amma ya sha alwashin tabbatar da kuɗin na yawo yadda zasu gamsar da bukatun yan Najeriya.

CBN ya yi zargin cewa wasu bankunan kasuwanci na ɓoye sabbin takardun naira da aka basu amma alamu sun nuna babban bankin bai buga wadatattun kuɗin ba.

A wani labarin kuma Babban Banki CBN Ya Musanta Barazanar Rufe Wasu Bankunan Ajiyar Kuɗi

Babban banki ya musanta manyan rahotonni biyu da ake yaɗawa game da sabon tsarin sauya fasalin naira a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Laifin 'Yan Najeriya Ne" CBN Ya Fasa Kwai, Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa Kan Karancin Sabbin Naira

A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, CBN ya ce ya shirya tsaf domin samar da isassun takardun kuɗi ga yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel