Babu Dan Takarar Da Zai Samu Kaso 70 Na Kuri’un Yan Arewa Amma Tinubu Ya Ci Zabe Ya Gama - Yakassai
- Babban jigo a arewa, Tanko Yakassai, ya yi hasashen yadda babban zaben 2023 za ta kasance yan kwanaki kafin gudanar da ita
- Yakassai ya ce za a yi raba daidai kuri'un yan arewa a tsakanin manyan yan takara don babu wanda zai samu kaso 70
- Dattijon kasar ya ce Asiwaju Bola Tinubu na APC ne zai zama magajin Shugaba Buhari idan har aka yi zabe na gaskiya
Dattijon Arewa, Tanko Yakassai, ya bayyana cewa babu dan takarar da zai samu kaso 70 cikin dari na kurin yan arewa.
Yakassai ya ce ana iya yin raba daidai kuri'un arewa a tsakanin manyan yan takarar shugaban kasa hudu.
Tinubu ne zai lashe zabe, Yakassai
Da yake magana a wata hira da jaridar Punch, dattijon ya ce babu abun da zai hana dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, cin zabe idan har aka yi shi cikin gaskiya da amana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yakassai ya ce:
"Abun da na yarda da shine cewa idan har aka gudanar da zaben cikin gaskiya da amana, babu abun da zai hana Tinubu, dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress, lashe zaben.
"Amma na ga wasu manyan masu ruwa da tsaki na nuna rashin amincewa da kudirinsa. Wasu daga cikinsu a APC suke kuma wasun su a jam'iyyun adawa.
"Abun da na yarda da shi shine cewa irin wadannan mutane idan suka gaza cin zabe, za su iya aikata magudi.
"Bana ganin akwai dan takarar da zai iya samun kaso 70 cikin dari na kuri'un arewa a zaben nan.
"Na san yawancin kuri'un za a raba shi daidai ne tsakanin yan takarar.
"Yan takarar da suka fito daga arewa, a nawa ra'ayin, ba kasafai suke hawa takardan zaben ba,
"Za su raba kuri'u a arewa kuma akwai yiwuwar kuri'un da Tinubu zai samu daga masu zabe a arewa zai dara na sauran manyan yan takara uku.
"Akwai mutane uku da aka ambata da suka kasance manyan yan takara. Akwai yiwuwar cewa za a raba kuri'un arewa gida da yawa.
"Idan hakan ya kasance, akwai yiwuwar cewa dunkulallun kuri'u za su tafi wajen Tinubu idan aka kwatanta da kowanne daga cikinsu. Yana iya samun kuri'u fiye da kowannensu."
Peter Obi na Labour Party, Rabiu Kwankwaso na New Nigeria Peoples Party (NNPP) da Atiku Abubakar na Peoples Democratic Party (PDP) suna cikin manyan yan takara a zaben shugaban kasa, rahoton The Cable.
DHQ ta yi watsi da ikirarin cewa Atiku ya hada kai da sojoji don yin juyin mulki a 2023
A wani labarin kuma, hedkwatar tsaro ta karyata rade-radin da ke yawo cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya hada kai da sojoji don yin juyin mulki a zaben 2023.
Asali: Legit.ng