Jami'Iyyar PDP Ta Zabi Sabuwar Ranar Zaben Fidda Dan Takarar Gwamna a Jihohi Uku

Jami'Iyyar PDP Ta Zabi Sabuwar Ranar Zaben Fidda Dan Takarar Gwamna a Jihohi Uku

  • Jam'iyyar PDP ta sauya ranar zaben fidda ɗan takarar gwamna a jihohin Imo, Kogi da kuma Bayelsa
  • Jihohin na daga cikin jihohi takwas da hukumar zabe mai zmaan kanta ta kasa ke gudanar da zaben gwamna a lokaci na daban
  • INEC ta tsara gudanar da zaben gwamna a jihohin guda uku ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023

Abuja - Jam'iyyar PDP fa ƙasa ta sanya sabuwar ranar tantance 'yan takara gabanin zaɓen fidda gwanin ɗan takarar gwamna na wajen tsari a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa canjin lokacin na ƙunshe ne a wata sanarwa da Sakataren tsare-tsaren PDP, Umar Bature, ya fitar ranar Jumu'a.

Tutar jam'iyyar PDP.
Jami'Iyyar PDP Ya Zabi Sabuwar Ranar Zaben Fidda Dan Takarar Gwamna a Jihohi Uku Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

A cikin sanarwan, jam'iyyar PDP ta ce zaben fidda gwanin, wanda aka shirya gudanarwa 13 ga watan Fabrairu, yanzu ya koma ranar 1 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Siyasa Ta Ɗau Zafi a Arewa, Kwamishinoni Sama da 10 Sun Fice Daga PDP Ana Gab da Zaɓe

Hak zalika babbar jam'iyyar adawan ta ce ta tsawaita sayar da Fom ɗin nuna sha'awa da shiga cikin manema takarar gwamna a jihar Kogi zuwa 13 ga watan Fabrairu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bugu da ƙari, jam'iyyar ta yi bayanin cewa ta tsawaita ranar ne saboda yawon yakin neman zaben shugaban kasa da ke gudana yanzu haka gabanin babban zaɓe.

"Wannan ɗan karin da aka samu ya zama wajibi saboda kakar kamfen da ake yanzu haka gabanin babban zaɓen 2023 mai zuwa."

"Dukkan sauran jihohin (Ban da Kogi) harkokin duk da suka shafi zaɓen fidda ɗan takarar gwamnan na nan yadda yake bai sauya ba," inji Sanarwan, kamar yadda Dailypost ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta gano cewa hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta tsara gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Karar Hana Peter Obi Takara a 2023

Waɗan nan jihohin guda uku na cikin jihohi Takwas da INEC ke gudanar da zabukansu a lokacin daban, sauran jihohin su ne, Anambra, Osun, Ondo, Ekiti da kuma Edo.

Kwamishinoni 11 Sun Fice Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC a Jihar Taraba

A wani labarin kuma Yayin da jirgin kamfen Tinubu ke shirin dira Taraba, Jam'iyyar APC ta samu ƙarin goyon baya

Rahotanni sun bayyana cewa ana sa ran shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da kansa zai karbi kwamishinoni 11 da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Wannan na zuwa mako biyu gabanin zaɓen shugaban kasa wanda zai gudana ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel