Wani Ya Shiga Katuwar Matsala a Kan Zargin ‘Danuwan Buhari da Ganin Bayan Tinubu

Wani Ya Shiga Katuwar Matsala a Kan Zargin ‘Danuwan Buhari da Ganin Bayan Tinubu

  • Kalaman Alwan Hassan a kan Sabi’u Tunde Yusuf sun jawo masa matsala, ana iya maka shi a kotu
  • Hadimin shugaban kasar ya nuna bai da hannu a zargin da ake yi masa na ganin bayan Bola Tinubu
  • Tunde ya bukaci afuwar Shugaban na kungiyar North-South Progressive Alliance ko dai su je kotu

Abuja - Sabi’u Tunde Yusuf wanda ‘danuwa ne kuma hadimi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karyata tuhumar da ake jifan shi da su.

A wani rahoto da The Cable ta fitar a yammacin Juma’a, za a ji Sabi’u Tunde Yusuf ya musanya cewa ya shiryawa jam’iyyar APC zagon-kasa a zaben bana.

Alwan Hassan ya yi hira a gidan talabijin kwanakin baya, a nan aka ji yana cewa hadimin na shugaban Najeriya ne yake yakar takarar Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ina son gaje kujerar Buhari: Tinubu ya nemi goyon bayan sarkin Musulmi, sarkin ya ba shi amsa

A cewar shugaban kungiyar North-South Progressive Alliance, duk wasu tsare-tsare na canjin kudi da aka fito da su, aikin Sabi’u Yusuf ne ba kowa ba.

Lauyoyi sun shiga maganar

A wata wasika da matashin ya aikawa Alwan Hassan a ranar 8 ga watan Fubrairu 2023, ya musanya zargin da yake yi masa, kuma ya dauki mataki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta ce Sabiu Yusuf wanda aka fi sani da Tunde ya aikawa Hassan wasika ne ta hannun kamfanin lauyoyinsa Wole Olanipekun & Co. ta yanar gizo.

Tunde Sabiu
Shugaban kasa da Tunde Sabiu Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

Lauyoyin sun ce wanda suke karewa ya nesanta kan shi daga zargin wanda aka rubutawa wasikar, su na zargin ikirarin da yake yi, ba gaskiya ba ne.

“Wanda mu ke karewa ya karyata zargin da ake yi masa a wata magana da ka yi, karya ne, sharri ne, kage ne kuma da gan-gan aka kitsa shi.

Kara karanta wannan

Abin da Zai Faru Idan Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa a 2023 – Gwamnan APC

Da alama ka yi wa wanda muke karewa wannan aiki ne saboda neman sharri, kiyayya da hassada.

Tunde yana neman diyyar N5bn

Wasikar lauyoyin ta kara da cewa zargin ya taba mukarrabin fadar shugaban kasar, ya jawo masa abin kunya da damuwa, kuma ya jefa shi a cikin barazana.

Tunde ya bukaci wanda aka rubutawa wasikar ya biya N5bn saboda bata shi da aka yi, sannan ya nemi afuwar shi a tashar talabijin nan da ya bata masa suna.

Lauyoyin sun nemi a wallafa afuwar a gidajen jaridu hudu da ake karantu su a fadin Najeriya, idan ba ayi wannan a kwanaki 21 ba, za a dauki mataki na shari’a.

Ado Bayero ya fada mani zan yi mulki - Atiku

A wani rahoto, an ji Alhaji Atiku Abubakar ya ce addu’ar da Marigayi tsohon Sarkin Kano, Ado Bayero ya yi masa tun can shekarun baya shi ne zai rike Najeriya.

Kara karanta wannan

Kasa Ta Yamutse, Shugaba Buhari Ya Kira Taron Gaggawa na Majalisar Koli a Najeriya

An ji Sarki Ado Bayero ya fadawa Atiku wannan ne a lokacin yana mataimakin shugaban kasa, ya ce Marigayin ya hange shi a kujerar shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng