Hadimin Gwamna Yahaya Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar APC Zuwa NNPP

Hadimin Gwamna Yahaya Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar APC Zuwa NNPP

  • Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya rasa ɗaya daga cikin manyan masu ba shi shawara ta musamman
  • Chokalin Waja, mai ba gwamna shawara kan yaɗa labarai da dabaru ya yi murabus daga mukaminsa kuma ya koma NNPP
  • Ya ce mukamin da aka ba shi jeka na yi kane amma ba shi da wani amfani a tafiyar da gwamnati

Gombe - Mai ba da shawara na musamman ga gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, Chokalin Waja, ya yi murabus daga mukaminsa kana ya sauya sheka zuwa NNPP.

Rahoton jaridar Tribune Online ya ce wannan na zuwa ne mako ɗaya bayan shugaban jam'iyyar NNPP a jihar ya tattara kayansa ya koma APC mai mulki.

Muhammad Inuwa Yahaya.
Hadimin Gwamna Yahaya Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar APC Zuwa NNPP Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Chokalin Waja, mai rike da rawanin sarauta a masarautar Balanga, an naɗa shi muƙamin mashawarci na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru a watan Disamban, 2022.

Kara karanta wannan

Siyasa Ta Ɗau Zafi a Arewa, Kwamishinoni Sama da 10 Sun Fice Daga PDP Ana Gab da Zaɓe

A ranar 7 ga watan Fabrairu, 2023, Mista Waja, ya sanar da sauka daga kan muƙamin a wata wasika da ya tura wa gwamnatin jihar Gombe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa ya dauki wannan matakin?

A cewarsa, ya ɗauki matakin sauka daga mukaminsa ne sakamakon yanayin yadda gwamnatin take watsi da dokoki da ƙa'idoji.

A kalamansa, Mista Waja ya ce:

"An naɗa ni a matsayin SA, idan muka yi la'akari da ƙunshin takardan aiki na, ni zan taimakawa gwamna kan batutuwan da suka shafi shugabanci wanda ya haɗa da yadda za'a kawo shugabanci mai kyau da dabarun cin zaɓe mai zuwa."
"Amma ba haka abun yake ba a zahiri, duk mutanen da aka naɗa jeka na yi ka ne kawai ba su da ta cewa a harkokin gwamnati, na gano kawai an bani muƙamin ne amma ba abinda zan yi."

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wike Ya Magantu Kan Hukuncin Kotun Koli, Ya Faɗi Matakin Da Zai Dauka Kan Sabbin Kuɗi

"Lamarin ya kai ga ko kaga ana kuskure ka yi magana, ba wanda zai saurare ka ko ya ɗauki shawarinka. Ko albashin da aka yanka mun bai taka kara ya karya ba a matsayin mai rike da mukamin siyasa."

PDP ta samu matsala a jihar Taraba

A wani labarin kuma awanni gabanin ralin Tinubu, Kwamishinoni 11 Sun Fice Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC a Jihar Taraba

Rahotannin da muka samu daga jihar da ke shiyyar da Kashim Shettima ya fito sun nuna cewa ana sa ran Buhari da kansa zai tarbe su.

Guguwar sauya sheka na ci gaba da cin kasuwa a arewacin Najeriya yayin da ya rage 'yan kwanaki zaben shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel