Wike Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Sake Amincewa Atiku Ya Yi Kamfe a Ribas

Wike Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Sake Amincewa Atiku Ya Yi Kamfe a Ribas

  • Gwamna Nyesom Wike ya yi amai ya lashe, ya sake baiwa kwamitin kamfen Atiku damar amfani da filin Adokiye Amiesimaka
  • A kwanakin baya, gwamnatin Ribas ta soke amincewa Atiku kamfe a filin wasan saboda wasu dalilai masu karfi
  • A ranar Talata, gwamna Wike ya ce bayan wasu manyan mutane sun nemi alfarma ya amince su Atiku su yi kamfe a filin

Rivers - Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya ce gwamnatinsa ta sake sahale wa jam'iyyar PDP ta ƙasa ta yi amfani da katafaren filin kwallon Adokiye Amiesimaka yayin kamfen Atiku Abubakar.

Channels tv tace a ranar 31 ga watan Janairu, 2023, gwamnatin Wike ta soke ba da Filin ga kwamitin kamfen Atiku, wanda ya shirya rali ranar 11 ga watan Fabrairu.

Gwamna Wike da Atiku.
Wike Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Sake Amincewa Atiku Ya Yi Kamfe a Ribas Hoto: channelstv
Asali: UGC

Gwamnatin Ribas ta bayyana cewa ta yi haka ne bayan samun bayanan sirri da kuma abinda ke faruwa a kwanan nan wanda ya nuna kwamitin kamfen Atiku ya haɗa kai da APC ta jihar.

Kara karanta wannan

Sauya Kudi: Da Gaske Gwamnan CBN Na Son Haddasa Rudani a Zaben 2023? Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Magantu

A cewarta, ta fahimci cewa kwamitin PCC-PDP ya shirya amfani da babban filin tare da jam'iyyar APC, jam'iyyar da harkokinta suka koma na ta da yamutsi da lalata kayayyaki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wike ya yi amai ya lashe

A halin yanzu, a wurin ralin PDP na ƙaramar hukumar Ogu/Bolo ranar Talata, Wike ya ce gwamnatinsa ta sake amince wa su Atiku su shiga Filin bayan wasu manyan mutane sun nemi alfarma.

Bayan haka, jagoran tawagar G-5 ya yi karin haske kan wasu batutuwa da suka shafi rigingimin cikin gida a babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP.

Shin gwamnan Abiya ya koma bayan Atiku?

Wike ya musanta kalaman shugaban jam'iyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, wanda ya yi ikirarin cewa ɗaya daga cikin gwamnonin G-5 ya kai masa ziyara har gida.

Gwamnan Ribas yace zancen ƙarya ne domin babu ɗaya daga cikin gwamnoni 5 da zai ziyarci Ayu yayin da suke fafutukar neman shugabancin jam'iyya ya koma hannun ɗan kudu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Budewa Tsohon Ministan Buhari Wuta, Mutum Biyu Sun Mutu

A cewarsa babu wanda zai yaudari gwamnonin G-5 ta hanyar nuna goyon baya a gaban jama'a, saboda yaƙi ne da suka fara wanda tabbas zasu ci nasara, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Gamu da Cikas a Edo, Mambobi 3,000 Sun Koma Jam'iyyar PDP

Rahotanni sun ce masu sauya shekar dun yaga katin mamban APC kuma sun lashi takobin tabbatar da PDP ta samu nasara manyan zabukan dake tafe.

Mafi yawan yan siyasan sun kafa hujjar cewa ba zasu ci gaba da zama a jam'iyar da ta kakaba masu talauci da wahalhalu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262