Yan bindiga sun kara kaiwa dan takarar jam'iyyar PDP Hari A Imo
- Yan bindiga sun sake komawa gidan jami'in hulda da jama'a na gamayyar jam'iyyun siyasa (CUPP), Ikenga Ugochinyere
- A watan Janairun da ya shige, maharan suka kashe kawun ɗan siyasan da wasu mutane uku kuma suka kone gidansa da motocinsa
- Wannan shi ne karo na biyu da 'yan bindiga suka kai masa hari, kuma ya ce sun je da muggan makamai yau Talata
Imo - Wasu tsagerun 'yan bindiga da ba'a san su ba sun sake kaiwa mai magana da yawum gamayyar jam'iyyun siyasa (CUPP), Ikenga Ugochinyere, kazamin hari har gida ranar Talata 7 ga watan Fabrairu.
Wannam sabon harin ya faru ne makonni uku bayan an kai masa makamancin wannan harin a garin Akokwa, jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Jaridar Punch ta tattaro cewa a ranar 14 ga watan Janairu, 2023 a Akokwa, jihar Imo, wasu yan bindiga a kan Babura suka kai hari gidan Ugochinyere, suka kona gidan da Motocinsa na hawa.
Bayan haka 'yan ta'addan ba su tsaya iya nan ba, sai da suka kashe kawum ɗan siyasan tare da wasu mutane uku a harin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tun a wancan lokacin ɗan siyasan ya bayyana halin da yake ciki game da harin 'yan bindigan kuma ya nemi mahukunta da su kawo masa ɗauƙi.
Mista Ugochinyere, shi ne ɗan takarar majalisar tarayya a mazaɓar Ideato ta arewa da Ideato ta kudu karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa.
Sabon harin yau Talata
A ranar Talata (yau) a wani gajeren sako da ya aike wa 'yan jarida ta manhajar Whatsapp, Mista Ugochinyere, ya sake ankarar da cewa wasu mutane dauke da bindigu sun kai masa hari.
Ya ce:
"SOS, yanzu haka an sake kai mana hari, yan bindiga sun farmaki gidana ɗauke da abubuwan fashewa kuma sun buɗe wuta ta ko ina."
Wata majiya ta bayyana cewa wannan sabon harin ya jefa fargaba da tsoro a zuƙatan tawagar yakin neman zaɓen ɗan siyasan, Sahara Reporters ta rahoto.
Duk wani yunkuri na jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Imo bai kai ga nasara ba har zuwa yanzu da muke haɗa wannan rahoton.
A wani labarin kuma ‘Yan Daban Siyasa Sun Kai Hari Ana Taron Jam’iyyar PDP, An Raunata Mata da Matasa
Wasu rahotanni sun bayyana cewa kalla mutane biyar suka jikkata yayin wasu 'yan daba suka kai haro gidan wani mutumi a jihar Gombe ranar Asabar.
An ce mutumin ya tara mata da matasa a gidansa domin sanar matakin da ya ɗauki na sauya sheka daga APC zuwa PDP, kwatsam aka farmake su.
Asali: Legit.ng