Karancin Naira: Ma'aikatan Banki Sun Arce Ta Katanga Yayinda Matasa Suka Far Musu

Karancin Naira: Ma'aikatan Banki Sun Arce Ta Katanga Yayinda Matasa Suka Far Musu

  • Ma'aikatan wani banki a Najeriya sun fara haura katanga tsoron abubuwan da ka iya afkawa kansu
  • Kwastomonin bankin na cikin wahalar karancin tsabar kudi bayan an kwace musu tsaffin kudadensu
  • Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu game da wannan bidiyon inda wasu ke musu dariya

Bidiyon wasu ma'aikatan bankin Zenith ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun haura katanga don su arce yayinda kwastomomi ke kokarin afka musu don amsan kudinsu.

Hakan ya biyo bayan rashin isassun takardun kudi cikin al'umma duk da wa'adin kwanaki 10 da gwamnati ta kara.

Tsarin sauya fasalin kudi da bankin CBN ya kawo ya jefa yan Najeriya cikin kunci da tsadar rayuwa.

Zentin
Karancin Naira: Ma'aikatan Banki Sun Arce Ta Katanga Yayinda Matasa Suka Far Musu Hoto: Leadership
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

"Yanzu Yan Boko Haram Sun Koma Sanya Tufafin Mata Yayin Kai Hare-Hare" - Inji Ndume

A wannan bidiyon, an ga ma'aikatan bankin suna hawa kan tsani domin guduwa kada a far musu.

Ana jin daya daga cikinsu na tambaya ko jami'an yan sanda sun iso.

Bidiyon ya tayar da cece-kuce a kafafen ra'ayi da sada zumunta.

Kalli bidiyon:

Ku Cigaba da Bin Layi Ba Zamu Kara Wa'adin Naira Ba Bayan Ranar 10 ga Febrairu, Gwamnan CBN

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa ba zasu sake daga ranar karse na daina amfani da tsaffin takardun Naira ba.

Emefiele ya bayyana hakan ranar Juma'a yayin hira da manema labarai a ofishin bankin dake jihar Legas.

Ya bayyana cewa suna iyakan kokarinsu domin magance matsalar karancin sabbin takardun kudin da jama'a ke fama da shi.

A cewarsa:

"Ina son in kara fada muku cewa wannan karon gaskiya ba mu tunanin dage wa'adin saboda mu a babban banki da kuma sauran bakuna muna iyakan kokarin don magance matsalan."

Kara karanta wannan

"A Soke Wannan Zaben Ayi Sabon Lale" Kwamitin Kamfen Atiku Ya Yi Kira Ga INEC

Ya yi kira ga yan Najeriya su cigaba da bin layi kuma suyi hakuri saboda amfanin sauyin fasalin Nairan ya rinjayi wahalar da suke sha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel