Zaben 2023: Tsohon Dan Majalisar Tarayya, Shehu Sani Ya Yi Tsokaci A Kan Masu Juya Aso Rock

Zaben 2023: Tsohon Dan Majalisar Tarayya, Shehu Sani Ya Yi Tsokaci A Kan Masu Juya Aso Rock

  • Maganganu akan ma su juya fadar shugaban kasa ta sake kunno kai
  • Tsohon Sanatan ya nemi dalilin da yasa har yanzu anki bayyana wadannan mutane inda ya wallafa a shafinsa na Twitter
  • Sanata Sani ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa akwai yiwuwar mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, yana cikin ‘yan cabal din

Twitter - Sanata Sani ya tambayi dalilin da ya sa ‘yan siyasa ba za su iya bayyana sunayen masu juya Aso Rock ba, a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Tsohon sanatan ya tafi sahihin shafinsa na Twitter ya yi tambaya kan abin da yasa yana da wahala yan siyasa da ke rike da mulki su ambaci sunan masu juya akalar gidan gwamnatin.

Sanata Shehu Sani
Zaben 2023: Tsohon Sanata, Shehu Sani Ya Yi Tsokaci A Kan Masu Juya Aso Rock. Hoto: Shehu Sani
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Babu laifin Buhari, Peter Obi ya ce 'yan Najeriya su hankalta, su yiwa Buhari uzuri

Sanatan ya wallafa a shafinsa na Twitter kamar yadda Legit.ng ta ruwaito a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairu, ya ce:

"Cabal din na da karfin ikon da ba wanda ya isa ya bayyana sunayensu. Ina zargin, ko dan uwana Femi Adeshina yana cikin Division 2 Cabal?"

Abin da shugabannin jam'iyyar APC suka fada game da su

A yan kwanaki gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi ‘yan cabal din da yin zagon kasa ga takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

El-Rufai ya bayyana cewa ’yan takarar shugaban kasa da suka sha kaye a hannun Tinubu a zaben fidda gwani na jam’iyyar ne ke haddasa rikicin da ya shafi jam’iyyar da kuma yakin neman zaben shugaban kasa.

Femi Fani-Kayode, jigo a jam’iyyar APC, ya amince da ikirarin gwamna El-Rufai na cewa wasu dakaru ne ke haddasa karancin sabbin naira da kuma rikicin da ke cikin jam’iyyar APC mai mulki a kasa.

Kara karanta wannan

Magana ta Fara Fitowa: El-Rufai Ya Yi Karin Haske Kan Manyan da ke Yakar Takarar Tinubu

Har yanzu dai ba a san ko su wanene su a fadar shugaban kasar da ke Abuja domin babu wanda ya fito ya bayyana hakan.

Naja'atu Mohammed ta ce Aisha Buhari na cikin masu juya fadar shugaban kasa

A bangare guda, Naja'atu Mohammed, tsohuwar mataimakiyar direkta a kwamitin yakin neman zaben Asiwaju Bola Tinubu ta zargi Aisha Buhari, matar shugaban kasa da kasancewa cikin masu juya fadar shugaban kasa wato, 'cabal'.

A cewar Naja'atu, Aisha Buhari ta dade tana shirya makarkashiya a fadar shugaban kasar tun bayan da Buhari ya hau mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel