Zaben 2023: Ku Amshi Kudinsu Amma Ku Zabe Ni, Peter Obi Ya Fada Wa Yan Najeriya

Zaben 2023: Ku Amshi Kudinsu Amma Ku Zabe Ni, Peter Obi Ya Fada Wa Yan Najeriya

  • Dan takarar jam'iyyar Labour, Mr Peter Obi ya shawarci masu zabe a Ilorin cewa su karbi kudin yan APC da PDP amma kadu su zabe su
  • Obi ya fada wa masu zaben cewa dama kudin da yan siyasan za su zo su raba musu kudin yan kasa ne saboda hakan su karba su kalmashe a aljihu
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya fada wa magoya bayansa cewa kada su yarda a rude su da addini, kabilanci, yana mai cewa gwamnatinsa za ta hada kan Najeriya

Ilorin, Kwara - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, LP, ya yi kira ga yan Najeriya su jefa masa kuri'a a zaben wannan watan, Daily Trust ta rahoto.

Obi ya yi wannan rokon ne lokacin da shi da abokin takararsa, Datti Baba-Ahmed, suka kamfe a Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Saraki Ya Magantu Kan Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Ya Fada Ma Yan Najeriya Abun da Za Su Yi Wa APC

Peter Obi
Zaben 2023: Ku Amshi Kudinsu Amma Ku Zabe Ni, Peter Obi Ya Fada Wa Yan Najeriya. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan takarar na LP sun isa Metropolitan Square, wurin ralli din tare da matansu da jagororin jam'iyyar.

Kudin ku ne, ku karba idan sun baku amma ku zabe jam'iyyar LP, Peter Obi

A cewarsa:

"Muna da sandan siddabaru da za mu canja Najeriya. Muna bukatar shugabanni da za su hada kan Najeriya, wannan shine alkawarin mu na farko. Za a iya samar da sabuwar Najeriya karkashin jam'iyyar Labour. Ba mu son Najeriya da macizai da akuyoyi ke hadiye kudi.
"Zaben wannan shekarar, za su zo muku da batun addini, kabila ko kudi, amma ku fada musu kuna jin yunwa. Ku karbi kudin da za su baku saboda kudin ku ne kuma ku zabe mu.
"Za mu iya gina Najeriya inda kowa zai yi farin ciki. Sun yi kamfe da lema da tsintsinya na fiye da shekaru 16 amma ba abin da suka haifar sai rashin tsaro da talauci. Wannan lokacin matasa ne. Yanzu ku tafi ku zabi alamar mu, mahaifi, mahaifiya da da don sada siyarsar jam'iyya da mutane."

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Babu laifin Buhari, Peter Obi ya ce 'yan Najeriya su hankalta, su yiwa Buhari uzuri

Ya ce tikitinsa tare da Baba-Ahmed zai tabbatar da cewa matasa sun samu muhimmin matsayi a kasar kuma ya bukaci su tattaro kansu don zaben.

Obi da tawagarsa, tunda farko sun ziyarci Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari a fadarsa.

Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Jam'iyyun Siyasa 10 Sun Mara Wa Atiku Baya a Jihar Anambra

A baya mun kawo muku cewa Farfesa Obioro Okonkwo, direkta a kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa ya ce jam'iyyu 10 a jihar Anambra suna goyon bayan takarar shugabancin kasa na Atiku Abubakar.

Okonkwo ya furta hakan ne yayin zantawa da yan jarida bayan kammala tattaunawa da yan kwamitin yakin neman zaben da aka yi a hedkwatar su da ke Awka kamar yadda Nigerian Tribune ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164