Zaben 2023: Tafiyar Atiku Ta Kara Karfi Yayin Da Jam'iyyu 10 Suka Goyi Bayansa A Jihar Peter Obi

Zaben 2023: Tafiyar Atiku Ta Kara Karfi Yayin Da Jam'iyyu 10 Suka Goyi Bayansa A Jihar Peter Obi

  • Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a Anambra ya bayyana cewa Atiku ne zai lashe zabe a Anambra
  • Okonkwo wanda babban darakta ne a kwamitin yakin neman zaben Atiku yace PDP ta saba lashe Anambra da kuma Kudu maso Gabas kuma hakan bazata chanja ba
  • Ya kuma bawa yan Najeriya tabbacin cewa halin kuncin da suke ciki zai zama tarihi da zarar Atiku ya karbi ragama

Anambra - Babban daraktan yakin neman zaben Atiku/Okowa a Anambra, Professor Obioro Okonkwo, ya ce akalla jam'iyyu 10 ne suka janye takara don marawa dan takarar PDP, Atiku Abubakar da mataimakin sa, Sen. Ifeanyi Okowa, a babban zaben shugaban kasa na 2023.

Okonkwo ya bayyana haka ga yan jarida jim kadan bayan kammala tattaunawar kwamitin yakin neman zaben daya gudana a babar hedikwatar kamfen a Akwa, ranar Juma'a, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu Gida-gida: Yadda Aka Gudanar Gangamin Tallata Tinubu Da Shettima Har Gida Ga Mazauna Wata Jahar Arewa

Atiku Abubakar
Zaben 2023: Tafiyar Atiku Ta Kara Karfi Yayin Da Jam'iyyu 10 Suka Janye Masa Takara A Fitacciyar Jihar Kudu. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce jam'iyyun adawa guda goma ne suka janye takara don goyon bayan takarar Atiku/Okowo, saboda sun san PDP ce zata lashe jihar da kuma Kudu maso Gabas kamar yadda ta saba kuma Anambra ita ce kan gaba a yankin; Abia, Enugu, Imo da Ebonyi duk sun shirya don a dawo da Najeriya hayyacin ta.

Ya ce sunyi ganawar ne don tabbatar da shirye-shiryen karshe kafin ranar zabe, rahoton PM Express.

Muna fatan samun nasara a zaben 2023, Farfesa Okonkwo

A cewar babban daraktan:

''Muna da yakinin yin nasara a Anambra. Mu mutane masu daraja wanda muka fuskanci meye siyasa da kuma kyakkyawar dimukradiyya.
''Baya ga dubban yan jam'iyyar adawa da suka dawo PDP a Anambra tun bayan da muka fara kira don ceto kasar nan, wasu jam'iyyu 10 sun karbi Atiku Abubakar da Sen. Ifeanyichukwu Okowa a matsayin yan takarar shugabancin kasa da mataimaki."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kwankwaso Ya Gana Da Atiku Sun Tattauna? NNPP Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

Ya cigaba da cewa:

''Muna da kwarin gwiwa a yunkurin mu na ceto Najeriya, alkawarin tabbatar da kasa daya, farfado da tsaro da tattalin arziki, da kuma sauran muhimman alkawura da Atiku yayi wa yan Najeriya, musamman Kudu maso Gabas.
''Don haka, zamu tabbatar sun yi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa, kamar ko yaushe jam'iyyar PDP zata ci gaba da yin nasara a Anambra."

Kwamitin ya kuma bada tabbacin cewa halin kuncin da Najeriya ke ciki a yanzu zai zama tarihi a satin farko da Atiku ya kama aiki a matsayin shugaban kasa, saboda zai kawo tsarin da al'umma zasu amfana.

Za ka iya yin nasarar zama shugaban Najeriya, Sarkin Katsina ya yi wa Atiku bushara

A wani rahoton kun ji cewa mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya yi wa Atiku Abubakar na PDP busharar cewa zai iya cin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: A Shirye Na Ka In Yi Aiki Tare Da Peter Obi Da Kwankwaso, Atiku

Sarkin ya furta hakan ne yayin karbar bakuncin Atiku a lokacin da ya ziyarce shi kafin tafiya wurin yakin neman zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel